Abubakar Shekau
Abubakar Shekau, an kuma sanshi da Darul Akeem wa Zamunda Tauhid, ko Darul Tauh woto (gidan tauhidi) (larabci دار التوحيد ), an haifeshi tsakanin 1967 ko 1975 (babu tabbaci) dan kabilar Kanuri ne kuma wanda akafi sani da shugaban kungiyar dan ta'addan Boko Haram, suke ikirarin kafa daular Musulunci a yankin Arewacin kasar. Kungiya ce ta masu tayar da bayar baya a Najeriya kamar yadda kasar ta ayyana ta sakamakon fitar da wani faifan bidiyo da Shugaban ta Shekau yayi ya nuna ikirarin kungiyar nayin mubaya'a ga kungiyar dake kokarin kafa daular musulinci a yankin gabas ta tsakiya wato (ISIS). Shekau ya rike matsayin mataimakin shugaban kungiyar a karkashin wanda ya kafa ta Muhammad Yusuf har zuwa lokacin da Yusuf ya rasa rayuwar sa a hannun jami'an tsaron kasar Najeriya a shekara ta dubu biyu da tara, 2009 inda daga bisani ya zama shugaban gungiyar har zuwa yanzu. Abubakar Shekau Musulmi ne kuma mabiyin akidar Sunni Islam ko Salafiyya.[1][2][3][4]
Abubakar Shekau | |||
---|---|---|---|
30 ga Yuli, 2009 - 20 Mayu 2021 ← Muhammad Yusuf | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Shekau (en) , 24 ga Maris, 1973 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Mutuwa | Dajin Sambisa, 20 Mayu 2021 | ||
Yanayin mutuwa | Kisan kai (suicide bombing (en) ) | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Hausa Larabci Kanuri Fillanci Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | soja | ||
Aikin soja | |||
Ya faɗaci |
Rikicin Boko Haram Tawayen Boko Haram, 2009 Ta'addancin Boko Haram a kamerun | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Bayanin Shekau
gyara sasheAsalin yaren haihuwa na Shekau shine Kanuri, amma kuma yana jin harsunan Hausa, Larabci, Filatanci da Turanci sosai. Yayi ikirarin cewa shi Musulmi ne kuma wanda yayi ilimin addinin na Musulunci na ainihi kuma mai bin akidar musulunci sauda kafa.
A faya fayan bidiyon da Shekau yake fitarwa a kafafen Yanar gizo yasha kalubalantar sojojin dake yaki da kungiyar sa cewa yafi karfin su kuma yananan kan agidar sa ta kafa daular Musulunci sannan bazasu iya dakatar dashi ba ko su kasheshi har sai in Allah ne ya kawo karshen rayuwar sa.
A wantan Yuni na 2012 hukumar kasar Amurka ta ayyana Shekau a matsayin dan ta'adda. Tun daga shekarar 2013 ne kasar ta Amurka tayi ikirarin bayar da ladan $7miliyan na dalar Amurka ga duk wanda ya taimaka wajen kama shekau. A wani karin kuma kasar Najeriya ma tayi ikirarin bayar da Naira miliyan 50 ga wanda ya taimaka wajen kama shekau din.
Shekau ya tsallake ma wani harbi da sojojin Najeriya suka yi masa a kafa a samamen da suka kai masa a shekarar 2009. Bayan ya tsallake rijiya da baya ne yaci gaba da kai hare-hare. A daya daga cikin sanannun hare-haren sa akwai wanda yayi garkuwa da yanmatan makarantar sakandare sama da 200 a 2014. Shekau yayi sanarwar cewar ya musuluntar da yanmatan dukkan su daga bisani kuma yayi barazanar yanmatan zasu rinka kai hare-hare kan Kiristoci.
A watan Augusta na sekarar 2016 gungiyar ISIS ta ayyana Abu Musab Al Barnawi a matsayin shugaban gungiyar ta boko haram kuma ya maye gurbin Shekau wanda yaki amincewa da hakan. Saidai daga baya Hukumomin tsaro na kasar ta Najeriya sun kama Albarnawi ranar 26 ga watan Disamba na 2016.
Rayuwar sa ta kashin kai
gyara sasheShekau dan Najeriya ne kuma yayi ikirarin shi haifaffen kauyen Shekau ne na jahar Yobe. Amma babu tabbaci game da adadin shekarun sa. Ya auri daya daga cikin matan Muhammad Yusuf.
Ana masa lakabi da Darul Tauhid wato Matattarar Kakaita Allah.
Raho tannin rasuwar sa daga bangaren gwamnati
gyara sasheSau tari bangaren gwamnatin taraiya tasha ikirarin cewar ta kashe Shekau, amma daga bisani sai ya fito a faifan bidiyo ya karyata maganar ta bangaren gwamnatin.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedfrance24-20120113
- ↑ "Boko Haram militant leader is dead, Nigerian military says". France 24 (in Turanci). 25 September 2014. Retrieved 19 February 2020.
- ↑ "Nigeria army claims death of Boko Haram leader". www.aa.com.tr. Retrieved 19 February 2020.
- ↑ Akinyelure, Didi (27 September 2016). "Dead or alive? The six lives of Boko Haram's leader". BBC News (in Turanci). Retrieved 19 February 2020.