Idi Barde Gubana

Dan siyasa a Najeriya

Alhaji Idi Barde Gubana (Shekarar haihuwa; 24 ga Afrilu 1960) ya kasance ɗan siyasa ne a Najeriya, wanda a halin yanzu shi ne mataimakin gwamnan Jihar Yobe na yanzu gwamna Mai Mala Buni da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a shekarar 2019. An haife shi ne a garin Gubana na ƙaramar hukumar Fune. Ya fito ne daga jinsin al'ummar Karai-Karai kuma shi ne ke riƙe da mukamin gargajiya na Wazirin Fune.[1]

Idi Barde Gubana
Deputy Governor of Yobe State (en) Fassara

2019 -
Rayuwa
Haihuwa Idi Barde Gubana, 24 ga Afirilu, 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen Karai-Karai
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Karatu gyara sashe

Barde, ya halarci makarantar firamare ta Daura a shekarar 1970 inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1976, sannan ya yi makarantar sakandare a kwalejin malamai ta Borno daga 1973 zuwa 1979 inda ya samu takardar kammala jarrabawar Afirka ta Yamma.[2] Ya yi makarantar koyon zamantakewar jama'a a Jos a shekarar 1989 don samun digirin HND. Daga nan sai ya tafi jami'ar Borno (UNIMAID) sannan ya yi digirinsa na farko a fannin kasuwanci (gudanar da kasuwanci) sannan ya tafi Jami'ar Tarayya dake Jihar Borno inda ya samu digiri na biyu a shekarar 2000. [3]

Aiki gyara sashe

Ya yi aikin koyarwa a shekarar 1980 a makarantar firamare ta Dawayya sannan kuma a matsayin shugaban makaranta a makarantar firamare ta Gubana a shekarar 1982 zuwa 1984. A 1982 ya yi aiki a sashen noma a Ƙaramar Hukumar Fune ta jihar Yobe. Ya rike mukamin shugaban sashen noma a sakateriyar ƙaramar hukumar Fika.[4]

Iyali da Addini gyara sashe

Barde ɗan Masarautar Gubana ne, yana da mata 3 da ’ya’ya 29, Sannan kuma shi musulmi ne.

Siyasa gyara sashe

Idi Barde ya fara tafiyar siyasarsa ne a shekarar 1997 a lokacin da ya tsaya takara kuma ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Fune ya zauna karkashin jam'iyyar tarayyar najeriya (United Nigeria Congress Party, UNCP), don wakiltar karamar hukumar Fune. A shekarar 2000 aka nada shi shugaban kwamitin riko a karamar hukumar Fune har sau biyu zuwa 2003. Ya zama mai ba da taimako na musamman a ayyuka na musamman ga gwamnan jihar Yobe Bukar Abba Ibrahim a shekarar 2007, bayan nan kuma aka nada shi a matsayin kwamishina ma’aikatar gaskiya da rikon amana da cigaban karkara ci gaban karkara. A shekarar 2008 ya zama mataimaki na musamman a taron kasa domin banbance, a karkashin Bukar Abba Ibrahim, sannan kuma ya kasance mataimakiyar dukiyar kasa a yankin arewa maso gabas karkashin jam'iyyar duk najeriya (All Nigeria Peoples Party, ANPP). A shekarar 2011 aka nada shi kwamishinan ma’aikatar noma ta jihar Yobe. An sake nada shi a matsayin kwamishinan ma’aikatar muhalli 2013, kwamishinan ma’aikatar kasafin kudi 2013, yayin da ayanzu yana matsayin mataimakin gwamnan jihar Yobe yafara 2019 zuwa yanzu.[5]

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.today.ng/topic/idi-barde-gubana
  2. https://www.channelstv.com/tag/alhaji-idi-barde-gubana
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-01. Retrieved 2022-01-01.
  4. https://dailypost.ng/2021/09/01/yobe-apc-fixes-first-week-of-september-for-lgs-congress
  5. https://nigeriaelections.stearsng.com/state/YB/governor/2019