Ibrahim Gaidam

Dan siyasar Najeriya

Ibrahim Gaidam ko Geidam (an haife shi a shekara ta alif 1956, a kauyen Bukarti) gwamnan jihar Yobe daga shekara ta 2009 zuwa shekara ta 2019, (bayan Mamman Bello Ali - kafin Mai Mala Buni).[1][2]

Ibrahim Gaidam
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023
District: Yobe East
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - Mayu 2023 - Bukar Ibrahim
District: Yobe East
gwamnan jihar Yobe

27 ga Janairu, 2009 - 29 Mayu 2019
Mamman Bello Ali - Mai Mala Buni
Rayuwa
Cikakken suna Ibrahim Gaidam
Haihuwa Jihar Yobe, 15 Satumba 1956 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party

Rayuwar shi ta farko da karatu gyara sashe

An haifi Gaidam a ranar 15 ga Satumba a shekara ta 1956 a kauyen Bukarti, karamar hukumar Yunusari a tsohuwar Borno, a yanzu jihar Yobe. Ya halarci Kwalejin Malamai ta Borno (BTC) Maiduguri daga 1974 zuwa 1979, inda ya samu takardar shedar koyarwa. Ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar 1981 zuwa 1983, inda ya yi Diploma a fannin lissafi. Daga baya ya koma Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya sami digiri na biyu (BSc) a fannin lissafi a shekarar 1990.

Aiki da Hidimomi gyara sashe

Ibrahim Gaidam tun farko shi akawunta ne ya yi aiki a ma'aikatun gwamnati da dama a tsohuwar jihar Borno kafin a rabata daga baya kuma ta koma jihar Yobe. Ya taɓa zama mataimakin daraktan kuɗi a hukumar kula da abinci da hanyoyi da ababen more rayuwa a karkara, ya kuma riƙe muƙaddashin daraktan kuɗi da samar da kayayyaki a ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta Yobe. Ibrahim Gaidam ya bar aikin gwamnati ne a shekarar 1995 lokacin da aka naɗa shi a matsayin kwamishinan matasa da wasanni, sannan kuma kwamishinan kasuwanci da masana’antu. Ya koma aikin gwamnati daga shekarar 1997 zuwa 2007 ya kasance Darakta a ma’aikatar kuɗi ta jiha da dai sauransu a shekarar 2009 Ibrahim Gaidam ya zamo Gwamnan jihar Yobe bayan rasuwar gwamnan sanadiyyar rashin lafiya ta ciwon Ƙoda.

Shiga Harkar Siyasa gyara sashe

A watan Afrilun, shekarar 2007, Ibrahim Gaidam ya zama Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe a Jam’iyyar ANPP, kuma an rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, shekarar 2007. An rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar a ranar 27 ga Janairu, shekara ta 2009 bayan rasuwar mai gidansa gwamnan Yobe a wancan lokacin. Gwamna Mamman Bello Ali ya rasu ne a Florida inda yake jinyar ciwon hanta. An naɗa Alhaji Abubakar Ali, dan uwa ga Mamman Ali a matsayin sabon mataimakin gwamna bayan da aka rantsar da Ibrahim Gaidam.

An nada Ibrahim Gaidam a matsayin shugaban kwamitin dabarun jam’iyyar ANPP a zaben shekara ta 2011. Biyo bayan tashin hankali da tarzoma da gungiyar Boko Haram mai tsatsauran ra'ayin addinin Islama ta tayar a cikin watan Yulin shekarar 2009 a Arewacin Najeriya, gungiyar gwamnonin Arewa (NGF) ta kira wani taron gaggawa a jihar Kaduna domin tattaunawa kan harkokin tsaro. A cikin gwamnoni goma sha tara na arewacin Najeriya, Mu’azu Babangida Aliyu na jihar Neja, Mohammed Namadi Sambo na Kaduna da Ibrahim Gaidam na Yobe ne kaɗai suka halarci taron kai tsaye. A watan Nuwamban shekarar 2009, Ibrahim Gaidam ya gabatar da sakon fatan alheri ga al’ummar Jihar Yobe a kan bikin Sallah Eid el-Kabir. A cikin jawabinsa, ya ja kunnen matasa kan yadda malaman addini masu son kai da masu yada jita-jita suke ingiza su a tashin hankali, inda ya yi tsokaci kan tashin hankalin da ya faru a watan Yulin shekara ta 2009. Ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmai da su haɗa kai da juna, su zauna lafiya da mabiya sauran addinai. a cikin ƙasar.

A ranar 26 ga watan Afrilu shekara ta 2011 an zaɓi Gaidam a matsayin gwamnan jihar Yobe karo na biyu. An kuma zaɓi Gaidam a ranar 11 ga Afrilu 2015 a karo na uku a matsayin gwamna. An zaɓi Geidam a matsayin Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas a Majalisar dattijan Najeriya ta 9th a ranar 23 ga Maris shekarar 2019.

Manazarta gyara sashe

  1. "Governor Ibrahim Gaidam of Yobe State". Nigeria Governors Forum. Retrieved 2 February 2022.
  2. "Gaidam sworn in as Yobe governor". Daily Trust. January 27, 2009. Archived from the original on July 8, 2011. Retrieved 2 February 2022.