BBC Hausa kafar yaɗa labarai a harshen Hausa ce, Mallakin tashar labarai ta BBC da turanci wato (British Broadcasting Corporation (BBC) World Service wadda take watsa shirye-shiryen ta a harshen Hausa musamman ma labarun da suka shafi ƙasashen Nigeria, Ghana, Niger da kuma sauran masu jin harshen Hausa dake a yankunan Yammacin Afrika. Bangare ne na harsunan da BBC ke watsa shiryeshiryen ta guda 33 wadanda guda 5 daga cikin su yarukan Afrika ne. Ana watsa shirye shiryen sashen na Hausa kai tsaye daga babbar tashar ta BBC dake birni Landan wato Broadcasting House da kuma tashar ta dake babban birnin taraiyar Najeriya Abuja dakuma shafinta na yanar gizo wanda ake wallafawa duka dai a birnin na Abuja[1]

BBC Hausa

Bayanai
Iri broadcast network (en) Fassara da Jaridar yanar gizo
Ƙasa Birtaniya
Tambarin BBC HAUSA

Tarihin BBC Hausa gyara sashe

Tashar BBC Hausa itace sashen farko da BBC ta fara gabatar,da shirye shiryen ta daga cikin harsunan dake Afrika kuma daya daga cikin biyar na harsunan Afrika da BBC ke watsa shirye shiryen ta. An kaddamar da tashar ne a ranar 13 ga watan Maris din shekara ta alif 1957 da karfe Tara da rabi 9:30 agogon GMT da shirin minti 15 wanda Aminu Abdullahi Malumfashi ya gabatar. Daga baya kuma Abubakar Tunau yacigaba da kawo labaran fassara a shirin BBC na Labarun yammacin Afrika wato West Africa in the News.[2] Ana gabatar da shirye shiryen sashin Hausa na BBC na farko farko a ranakun Laraba da Juma'a ne kawai, bayan shekara daya kuma akaci gaba da gabatar da labarun kullum kullum.ranar 1 ga watan Yuni shekara ta alif dari tara da Hamsun da takwas 1958.

A watan Mayu na 2017 ne BBC Hausa tayi bikin cika shekara ta sittin 60 da fara watsa shirye shirye. Bikin ya samu halartar daraktar BBC wato BBC World Service Group, Fran Unsworth.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya tura sakon murya a yayin bikin inda ya ambaci tashar ta BBC Hausa da tashar jan hankalin masu sauraro kuma wadda ta kwashe shekaru tana gabatar da shirye shirye.

Ofishin Abuja gyara sashe

Anbude Ofishin BBC Hausa a Abuja tun a shekarar 2002.

Watsa, shirye shirye gyara sashe

A yawancin lokuta BBC nada babban edita da masu gabatar da shirye shirye da mataimakan editoci da babban mai gabatar da rahoto. Sannan kuma tafi karfin gabatar da labarunta game da al'amuran da suka shafi biranen Kaduna, Kano, Jos, Enugu, Abuja da Sokoto da kuma kasahen Niger republic, Ghana da kasar Sin.[3]

Tashoshin FM da suke gabatar da shirye shiryen BBC Hausa a Najeriya gyara sashe

Ana sake watsa wasu shirye shiryen na BBC Hausa a kafafan Radiyo da Talabijin dake Najeriya da hadin gwiwar kafar BBC wato BBC World Service. Ga wasu daga cikin su[4]

Shiye shiryen kafar yanar gizo gyara sashe

 
Wasu daga cikin kafofin yanar gizo da ake sauraren bbc hausa kenan

Ana gabatar da shirye-shiryen sashen Hausa na BBC a kafar yanar gizo cikin kwarewa kuma da sauki wajen nemowa.[5] Kafar yanar gizon BBC Hausa ta zama kafa ta biyu wadda akafi ziyarta a Najeriya, da masu ziyarta miliyan 68.6 a wata (wasu da wayar hannu wasu kuma da kwamfuta wasu kuma da akwatun Rediyo). Da kuma mabanbantan masu siya miliyan 3.5 a kowanne wata. BBC Hausa nada mabiya masu dimbin yawa a kafafen sada zumunta. Kimanin sama da mutum 840,000 a Facebook, da mabiya sama da 100,000 a Twitter, da mabiya samada 70,000 a Googl+, da mabiya samada 6,600 a Youtube.[6]

Manazarta gyara sashe

  1. "Game da mu". bbc.com/hausa. BBC. Retrieved 23 September 2019.
  2. "BBC Hausa marks 60th anniversary with lectures". dailytrust.com.ng. Daily Trust. Archived from the original on 11 October 2017. Retrieved 23 September 2019.
  3. "Ma'aikatan Sashen Hausa". bbc.com/hausa/staff. BBC Hausa. Archived from the original on 15 December 2017. Retrieved 23 September 2019.
  4. "Abokan huldar BBC Hausa". bbc.com/hausa. BBC. Retrieved 23 September 2019.
  5. "Radio's Popularity Declining Unevenly". nytimes.com. The New York Times. Retrieved 23 September 2019.
  6. "BBC's Hausa service has started to host advertising". thenigerianvoice.com. The Nigerian Voice. Retrieved 23 September 2019.