Kasar Misra ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma ta na kudu maso yammacin Asiya [1]ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta a kan marar raba. ta kusa da nahiyar Turai, sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar Maliya.

Globe icon.svgMisra
جُمهورِيّةُ مِصرَ العَرَبيّةِ (ar)
Flag of Egypt (en) Coat of arms of Egypt (en)
Flag of Egypt (en) Fassara Coat of arms of Egypt (en) Fassara

Take Bilady, Bilady, Bilady (en) Fassara

Suna saboda Ptah (en) Fassara da Mizraim (en) Fassara
Wuri
EGY orthographic.svg
 27°N 29°E / 27°N 29°E / 27; 29

Babban birni Kairo
Yawan mutane
Faɗi 94,798,827 (2017)
• Yawan mutane 93.82 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Larabci
Labarin ƙasa
Bangare na Arewacin Afirka, Gabas ta tsakiya da Yammacin Asiya
Yawan fili 1,010,407.87 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Mediterranean Sea (en) Fassara da Nil
Wuri mafi tsayi Mount Catherine (en) Fassara (2,629 m)
Wuri mafi ƙasa Qattara Depression (en) Fassara (−133 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Kingdom of Egypt (en) Fassara da All-Palestine Government (en) Fassara
Ƙirƙira 28 ga Faburairu, 1922Kingdom of Egypt (en) Fassara
3150 "BCE"
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati jamhuriya
Gangar majalisa House of Representatives (en) Fassara
• President of Egypt (en) Fassara Abdul Fatah el-Sisi (8 ga Yuni, 2014)
• Prime Minister of Egypt (en) Fassara Moustafa Madbouly (en) Fassara (14 ga Yuni, 2018)
Ikonomi
Kuɗi Egyptian pound (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Suna ta yanar gizo .eg (en) Fassara da .مصر (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +20
Lambar taimakon gaggawa 122 (en) Fassara, 123 (en) Fassara da 180 (en) Fassara
Lambar ƙasa EG
Wasu abun

Yanar gizo egypt.travel
Tuta Misra
Taswirar Misra
Kasar masar
masar

Dalar Giza da ke birnin Al-ƙahirar Kasar. Misra ko ƙasar Masar dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin Al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun ƙarnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau ga ta a ƙarshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka idan aka yi la'akari da waɗannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin ƙasar Misra yake da ƴar rikitarwa.

Suma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin ruɗani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, duk kan waɗannan siffofi, siffofi ne da ba kasafai ya kamata a ce wata ƙasa guda ɗaya ta haɗa su ba. To sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan faɗin ƙasar yana ɓangaren nahiyar Afirka ne. To amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin sinai na ƙasar Misiran a matsayin ɓangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin ƙasar ne.

Kogin Nilu wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. A zamanin da can, dangantakar Misra da ƙasashen da ke Afirka na da matukar ƙarfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke ƙarƙashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a ƙarni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta fuskanta zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta, da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma ƴan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau kuma wasu dayawa daga cikinsu, kusan ace waɗanda suke su ne 'yan asalin ƙasar ta Misira, waɗanda kuma akafi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasalima suna iƙirarin su jinin Afirka ne.

masar

Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru 200 da suka gabata, Misra tana da alaƙa mai ƙarfi da ƙasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu ƙasashe da dama na nahiyar ta Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta ci gaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar yankin Gabas ta Tsakiya,yana daga cikin tarihi misra itace gari na farko a tarihi da sheɗan da kansa ya bayyana ga azzalumin sarki fir auna a lokacin da fir auna yace shine ubangiji.

TarihiGyara

Kasan tana da matukar tarihin gaske a yankin Afirka da duniya gabaki daya

Al'aduGyara

AbinciGyara

TufafiGyara

YarikaGyara

MulkiGyara

 
Gwamnatotin masar
 
Tarukan gwamnati a masar


 
Tarurrukan gwamnati a masar

Kasan misra tana da karfin mulki.


ArzikiGyara

NomaGyara

Kasan misra suna da dabino da fure daban daban.


Kiwon lafiyaGyara

Akwai asibitoci da'ake kula da marasa lapiya

WasanniGyara

AddiniGyara

MusulunciGyara

KiristanciGyara

TsaroGyara

ManazartaGyara


Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe