Wikipedia:Tutorial
Wikimedia help page (en) Fassara


Wikipedia:
Gabatarwa Rajistar account Yadda ake gyaran Wikipedia Yadda ake mahadar shafi Bada madogarar bincike Shafukan tattaunawa Manufofin Wikipedia Karin bayani  

Wannan shafukan dake tafe suna dauke da muhimman bayanai akan yadda ake gyeran Wikipedia.

Manufofin Wikipedia

Manufar Wikipedia shine ta tattaro ilimin bangarori da dama wanda ya shafi dukkan ilimin dan adam domin amfanar da al'umma. Dukkan bayanan dake akan Wikipedia dole ne ya zama gaskiya ne, sannan kuma an bada madogarar inda aka samo.

Wikipedia tana maraba da kowa, kuma tana ba kowa damar bada gudummuwar sa wajen wannan aiki.

Wikipedia tana da wasu manufofi sannan ita ba wuri bane na talla ba, kowace iri. Wikipedia tana bada bayani akan mutane sanannu a tarihi amma ba ta tallata su ba, hakazalika, kamfanoni, masa'na'antu, da duk wani abu da dan adam ya kintace a kundayen ilimi da aka riga aka rubuta.

Bidiyoyin da'akayi bayani akan Wikipedia

Wadannan bidiyoyin guda biyu, bidiyoyine da suke bayani akan Hausa Wikipedia da kuma Wikipedia a jimlatance, bidiyan farko bidiyo ne da wasu daga cikin kwararrun editocin Hausa Wikipedia suke bayani cikin hikima ta hanyar tambaya da kuma amsa akan Wikipedia da kuma Hausa Wikipedia, kuma suna bayanin ne a saukake a cikin harshen Hausa. Bidiyo na biyu kuma yana bayani ne akan ta hanyan da edita zai bi wajen yin editin a Wikipedia, wasu kwararrun editoci ne suke bayanin a cikin harshen Hausa.

Bidiyoyi na tutorial(Kirkiran mukala)

Wadannan bidiyoyi ne da zasu taimaka ma Hausawa sanin hanyoyin da zasu bi wajen gudanar da sauye-sauye da kuma gyara a Hausa Wikipedia, Bidiyoyin zasu taimaka ma sababbin editoci sanin hanyar da zasu bi wajen koyan editin cikin sauki a Wikipedia. Kowanne bidiyo a cikin nan yana da darasin da yake koyarwa, idan kana da bukatan karin bayani ko kuma neman wasu bidiyoyi, zaka iya ma wannan magana a shafin shi na tattaunawa Anasskoko. Wadannan bidiyoyin dake kasa bidiyoyi ne da zaka koya yanda ake kirkiran shafi/mukala wato (article) a Wikipedia.


Idan kai mutun ne ma'abocin karance-karance zaka iya duba PDF na koyan yanda zaka kirkira mukala a Hausa Wikipedia, ka sauke manhajar PDF din a cikin wayarka.


Bidiyoyi na tutorial

Wadannan wasu daga cikin bidiyoyi ne da su taimaka ma edita wajen sanin hanyar da zai bi wajen saka hoto a WP:Wikimedia Commons da kuma yanda saka hoto a mukala wato (article), da wasu bidiyoyi ma da zasu taimaka wajen koyama edita abubuwa da yawa.


Idan kuna bukatan wasu muhimman bayanai ku duba a wadannan shafukan Manufofi Biyar | Visual editor | Yadda ake rubuta muƙala | Rubutu a mahangar da ba son rai | Ingancin tushen bayanai


Ci gaba zuwa Rajistar account