Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Neja, Wanda aka fi sani da Niger poly, babbar makarantar koyarwa ce dake a Zungeru, Jihar Neja, Nijeriya.

Niger State Polytechnic

Bayanai
Iri ma'aikata
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 10 ga Janairu, 1977
hoton niger polytechnich

Tarihi da manufa gyara sashe

Cibiyar ta fara ne a matsayin Kwalejin Ilimi ta Zungeru (ZUCAS). Gwamnatin jihar ta kafa ZUCAS tare da Dokar Jihar Neja a shekara ta 1979 mai lamba 7, kodayake a zahiri ta fara aiki ne a ranar 10 ga watan Janairu shekara ta 1977 a wani wurin wucin gadi a Kwalejin Gwamnati, a Bida . A watan Satumba na shekara ta 1984 ma'aikatar ta koma matsayinta na dindindin wanda ke tsakanin Zungeru da Wushishi . Manufofin kwalejin shi ne samar da karatuttukan asali don shirya ɗalibai don buƙatun shiga jami'a, da ba da kwasa-kwasai a matakin ƙaramin digiri. Tsarin Ilimi na 6-3-3-4 a cikin Najeriya ya buƙaci a sake maimaita shi da daidaita yanayin matsayin Makarantun Kwalejin Nazarin Asali da Makarantun Koyon Ilimin Gaba. Ganin haka, sai gwamnatin jihar Neja ta hanyar Kammalawa mai lamba C 4 (11) ga Disamba 1990, ta amince da sauya ZUCAS zuwa (Niger State Polytechnic Zungeru). Bayan haka, Dokar Jihar Neja mai lamba 9 a shekara ta 1991 aka fara aiki daga 1 ga wayan Oktoba shekara ta 1991 don tallafawa.

Polytechnic yanzu tana aiki da tsarin kwaleji tare da manyan cibiyoyi biyu: Kwalejin Kimiyya da Fasaha (CST) a Zungeru, da Kwalejin Gudanarwa da Nazarin Kasuwanci (CABS) a Bida.[1]

Duba kuma gyara sashe

  • Jerin ilimin fasaha na poly a Najeriya

Manazarta gyara sashe

 http://www.polyzungeruonline.com Archived 2022-06-27 at the Wayback Machine

  1. "Gunmen kill Niger poly lecturer". Vanguardngr.Com. 31 January 2014. Retrieved 15 October 2021.