Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa
Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa (wanda aka fi sani da, Nasarawa State Executive Council a Turance) ita ce mafi girman hukuma wacce take taka rawa a cikin Gwamnatin Jihar Nasarawa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Nasarawa . Ta kunshi Mataimakin Gwamna, Sakataren Gwamnatin Jiha, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni waɗanda ke shugabantar sassan ma’aikatun, (tare da yardar bangaren majalisar dokoki na gwamnati) mataimakan na musamman na Gwamna.
Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Executive Council (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Applies to jurisdiction (en) | Nasarawa |
Ayyuka gyara sashe
Majalisar zartarwa ta wanzu don ba Gwamna shawara da jagorantar sa. Nadinsu a matsayin membobin Majalisar Zartarwa ya ba su ikon aiwatar da iko akan filayensu.
Jagoranci na yanzu gyara sashe
Majalisar Zartarwa ta yanzu [1] tana aiki ne a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule wanda aka rantsar a matsayin Gwamna na 6 na Jihar Nasarawa a ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta 2019. [2]
Ofishin | Mai ci |
---|---|
Gwamna | Abdullahi Sule |
Mataimakin Gwamna | Dr. Emmanuel Akabe |
Sakataren Gwamnatin Jiha | Muhammed Ubandoma-Aliyu |
Shugaban Ma’aikatan Gwamnati | Abari Aboki |
Shugaban Ma’aikata | |
Sakataren dindindin, Gidan Gwamnati | Hamza A. Gayam |
Babban Sakatare Mai zaman kansa | |
Kwamishinan Noma da Albarkatun Ruwa | Allananah O. Otaki |
Kwamishinan Kudi, Kasafin Kudi, da Tsarin tattalin arziki | Haruna Adamu Ogbole |
Kwamishinan Kasuwanci, Masana'antu & Zuba Jari | Boyi Obadiah |
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, da Fasaha | Fati J. Sabo |
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa | Musa I. Abubakar |
Kwamishinan Lafiya | Ahmed B. Yahaya |
Kwamishinan yada labarai, Al'adu da yawon bude ido | Dogo Shammah |
Kwamishinan Shari'a | Abdulkarim A. Kana |
Kwamishinan Kasa da Ci gaban Birane | Salihu LA Alizaga |
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu | Yusuf A. Turaki |
Kwamishinan Ayyuka na Musamman | Muhammad Abubakar Imam |
Kwamishina mai kula da harkokin mata da cigaban al’umma | Halima A. Jabiru |
Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri | Philip Dada |
Kwamishinan cigaban matasa da wasanni | Othman B. Adam |
Manazarta gyara sashe
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-03-25. Retrieved 2020-10-15.
- ↑ http://dailypost.ng/2015/09/30/nasarawa-elections-maku-loses-bid-to-unseat-al-makura/