Majalisar Ɗinkin Duniya

(an turo daga UN)

Majalisar dinkin Duniya :Dai tsari ne wanda kasashen duniya suka amince da kerawa domin magance rikice-rikice da yake faruwa bayan yakin duniya na Biyu (2). An kafa ta ne a shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da biyar (1945)domin samar da kwanciyar hankali a cikin duniya baki daya.

Majalisar Ɗinkin Duniya

Hymn to the United Nations (en) Fassara
Bayanai
Suna a hukumance
United Nations, 联合国, Organización de las Naciones Unidas, Организация Объединённых Наций, منظمة الأمم المتحدة, Organisation des Nations unies, Vereinte Nationen da Organizacja Narodów Zjednoczonych
Gajeren suna ONU, OSN, UN, БДО, PBB, BM, FN, YK, ONU, ÜRO, PBB, ONU, ООН, VN, ONZ, ANO, UN, UN, VN, 国連, או"מ, ONI da BMT
Iri intergovernmental organization (en) Fassara da international organization (en) Fassara
Ideology (en) Fassara internationalism (en) Fassara
Aiki
Bangare na United Nations System (en) Fassara
Ƙaramar kamfani na
Mulki
Shugaba António Guterres
Sakatare António Guterres
Mamba na board
Hedkwata New York
Subdivisions
Tsari a hukumance intergovernmental organization (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 24 Oktoba 1945
1945
Wanda ya samar
Wanda yake bi League of Nations (en) Fassara
Awards received

un.org


gini Majalisar Ɗinkin Duniya
majalisar dinkin duniya
Majalisar dinkin Duniya

Kuma ta kunshi kusan dukkanin kasashen duniya, banda kasashe biyu; palestinu da Saint-siege. Muhimmin, Jawabin da Majalisar dinkin duniya ta bayyana game da Hakkokin 'Yan-adam a shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da takwas 1948.

Tarihin Majalisar dinkin Duniya:

gyara sashe

Koda yake kafin kafuwar Majalisar ta dinkin Duniya akwai wasu kungiyoyi da aka kafa domin hadin kai da cigaban kasashen duniya, irin su kungiyar ma'aikatan sadarwa ta kasa da kasa a shekara ta alif dubu daya da dari takwas da sittin da biyar 1865, da kuma kungiyar ma'aikatan gidajen wasilu a shekara ta alif dubu daya da dari takwas da casa'in da hudu 1874. Wa'yanda daga bisani suka rikide zuwa hukumomin Majalisar ta dinkin Duniya bayan da aka kafa ta.

Taron farko da aka gudanar a karkashin lemar Majalisar dinkin Duniya itace wanda aka gudanar a birnin Hague. Wannan taro dai shine yakai ga kafa kotun duniya dake birnin na Hague a kasar Holland a shekara ta alif dubu daya da biyu (1902)

A shekara ta alif dubu daya da dari tara arba'in da biyar (1945) ne kasashen duniya hamsin (50) suka gudanar da taro a Jihar San Francisco na Amurika domin kaddamar da dokoki ko jadawalin aiyukan ta Majalisar dinkin Duniya. Manyan ƙasashen duniya da suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar dai sun hada da Amirka da China da Tarayyar Rasha da Birtaniya da kuma Faransa, wa'yannan kasashen ne kuma daga bisani suka zama wakilai na dindindin na masu karfin fada aji.

A ranar ashirin da hudu (24) ga watan Oktoban shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da biyar (1945) ne dai wa'yannan kasashe suka rattaba hannu a daftarin karshe da ya kafa Majalisar ta dinkin Duniya, abinda ma yasa a duk ranar ashirin da hudu (24)ga watan na oktoba Majalisar ke bikin zagayowar ranar da aka kafa ta. Kuma a bana Majalisar ta cika shekaru sittin da hudu(64) da kafuwa. Kuma tun bayan kafuwan ta tayi shugabanni da dama kuma na baya bayan nan sune Butrus Butrus Ghali daga Masar da Kofi Annan na Ghana da kuma maici yanzu Ban Ki-Moon daga ƙasar Koriya ta Kudu. [1]

 
Tambarin Majalisar Ɗinkin Duniya
 
Majalisar Ɗinkin Duniya
 
  Membobin Majalisar Dinkin Duniya
  Jahohin Masu Sa ido na Majalisar Dinkin Duniya (Palestine, Vatican)
  kasashen da ba mamba ba (Niue, Cook Islands)
  kasashen Masu Mulkin Kai
  Antarctica (yankin duniya)

Manazarta

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe