Iran tazama Jamhuriyar Musulumci a shekara ta 1979 bayan khomeini ya kwace mulki daga Mohammad Reza Pahlavi. shi'a ne mafi yawan akidun mutanan kasar. Sedai akwai mabiya sunnah da wasu addinan kaman Kiristanci da zardtosht.
Adadin al'umman Iran sunkai kimanin 74,000,000 Mabiya Akidar shi'a sune mafiya Yawa Akasar. Ahlus Sunna Kuwa Yawansu Bai Wuce adadin mutane 20,000,000 ko 25,000,000 daga kabiloli daban daban kamar turkumawa , kablwshawa, da kurdawa.yawan kurdawa zasu kai 10,000,000 zuwa 12,000,000 dukkanin su yan ahlus-sunnah ne.
Ranakin hutu
Sallar cikar shekaran farisawa da ta kurdawa ranar 21 ga watan Maris wannan salla ce mai muhimmanci garesu
Tarihi ya nuna cewa kafin shekara ta 1000 makiyayan Farisa da kabilar Kurdawa sune mutanen farko wa'yanda suka zauna a Iran , tun a shekara ta 500 kafin haifuwar Annabi Isah, Farisa ta kamu da yakin basasa da juyin juya hali na mulki a wannan shekara inda turawa suka mamaye kasar, suka sa hukunci me tsanani tun daga wannan lokacin kasar ta samu kanta a babbar matsala , a shekara ta 612 kafin haihuwar Annabi Isah, Ashurawa suka kwace mulkin kasar bayan sun kwace mulkin kasar.
Tsarin gwamnati da dokokin Iran tsarin musulunci ne na shi'a kuma suna bin dimokradiya suna zabin shugaba a kowace shekara hudu (4) shugaban Iran yana iya ya shiga zabe sau biyu kadai tsarin siyasar Iran tana kama da tsarin Amurka, Iran tana adawa da Amurka da Isra'ila sosai.
↑A. Fishman, Joshua (2010). Handbook of Language and Ethnic Identity: Disciplinary and Regional Perspectives (Volume 1). Oxford University Press. p. 266. ISBN978-0-19-537492-6. " "Iran" and "Persia" are synonymous" The former has always been used by the Iranian speaking peoples themselves, while the latter has served as the international name of the country in various languages