Lardunan Najeriya
Lardunan Nijeriya sun kasance rarrabuwar yankuna a Najeriya, an yi amfani da yankunan daga 1900 zuwa 1967 a lokacin Mulkin Mallaka na turawa a Najeriya da kuma jim kaɗan bayan samun ƴancin kai a ƙasar. An canza su sau da yawa ta tarihinsu. An raba su kashi kashi; wasu daga cikin waɗannan an ƙara raba su zuwa hukumomin ƙasa. Arewacin Najeriya da Kudancin Najeriya suma wani lokaci ana kiransu da Lardunan Arewa ko kuma Kudancin Najeriya. A halin yanzu, Najeriya tarayya ce da ta ƙunshi jihohi 36.
Lardunan Najeriya |
---|
An fara amfani da larduna a Arewacin Najeriya bayan da Birtaniyya ta karɓi ragamar tafiyar da yankin daga hannun Kamfanin Royal Niger a shekarar 1900. Da farko Turawan Ingila sun raba yankin zuwa larduna goma sha daya wadanda su ne:
A cikin 1903 an ƙara ƙarin larduna shida; biyar bayan yaƙin Sokoto - Kano, da kuma lardin Gwandu, wanda ya kai 17. An rage yawan larduna zuwa 13 a shekara ta 1911, da kuma 12 bayan yakin duniya na daya. A 1926 Adamawa da Plateau sun zama sabbin larduna. Larduna da sassa a cikin 1945, tare da sunaye ko adadin Hukumomin Ƙasa a kowane yanki:
Akwai larduna goma sha uku a Arewacin Najeriya a shekarar 1966 da kuma aka soke a watan Mayun 1967: