Birgediya (Rundunar Sojin Sama) Musa Usman shi ne gwamnan farko a jihar Arewa maso Gabashin Najeriya daga watan Mayu 1967 zuwa Yuli 1975 bayan an kafa jihar daga wani yanki na Arewa a lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.[1]

Musa Usman
Gwamnan Jihar Borno

28 Mayu 1967 - ga Yuli, 1975 - Muhammadu Buhari
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Kanuri
Harshen uwa Kanuri (en) Fassara
Karatu
Makaranta Royal Military Academy Sandhurst (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar

Usman ya halarci Royal Military Academy Sandhurst, Ingila inda ya samu kwamishina a 1962.[2] Manjo Usman ya kasance dan takara a juyin mulkin Yuli 1966 lokacin da aka hamɓaar da Manjo Janar Aguiyi Ironsi, aka maye gurbinsa da Janar Yakubu Gowon.[3] Usman wanda aka naɗa a matsayin gwamnan jihar Arewa maso Gabas a watan Mayun 1967, ya fara aikin gina masana'antar siminti ta Ashaka, wanda Manjo-Janar Shehu Musa 'Yar'aduwa ya buɗe a ranar 19 ga Yuli 1979.[4] A shekarar 1975 ya shiga tattaunawar sada zumunci da Kamaru don daidaita kan iyakar ƙasar da Najeriya.[5] Ya kasance mai goyon bayan ƙa'idar da ya kamata gwamnatin soja ta mika wa farar hula a 1976.

Musa Usman

Bayan ya yi ritaya sai aka ba shi masauki a Unguwar Jabi Street Kaduna . Daga baya Usman ya zama darakta a bankin Arewa.

Manazarta

gyara sashe
  1. Nowa Omoigui. "OPERATION 'AURE': The Northern Military Counter-Rebellion of July 1966". Africa Masterweb. Archived from the original on 2008-07-23. Retrieved 2010-05-15.
  2. "History". Ashaka Cement Works. Archived from the original on 2010-01-30. Retrieved 2010-05-15.
  3. Nowa Omoigui. "OPERATION 'AURE': The Northern Military Counter-Rebellion of July 1966". Africa Masterweb. Archived from the original on 2008-07-23. Retrieved 2010-05-15.
  4. "History". Ashaka Cement Works. Archived from the original on 2010-01-30. Retrieved 2010-05-15.
  5. http://repository.unn.edu.ng/index2.php?option=com_docman&task=doc_view&gid=1428&Itemid=306[permanent dead link]