Atiku Abubakar
Atiku Abubakar'Atiku Abubakar (Taimako·bayani) (an haife shi a ranar 25 ga watan Nuwamba shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da shida, 1946)[1] Miladiyya. Ya kasance dan siyasan Najeriya,kuma dan kasuwa ne wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar Najeriya daga shekara ta alif Dari Tara da casa'in da tara , 1999 zuwa shekara ta 2007 lokacin shugabancin Olusegun Obasanjo.[2][3][4] Atiku ya nemi zama gwamnan Jihar Adamawa a shekara ta alif, 1990 zuwa 1996 daga baya kuma, a shekara ta alif, 1998, aka zaɓe shi kafin nan ya zama mataimakin Olusegun Obasanjo[5] a Zaben shekarar, 1999 na shugaban kasar Najeriya an kuma sake zaben su a zaben shugaban kasar Najeriya ta 2003.[6]
Atiku Abubakar | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Mike Akhigbe - Goodluck Jonathan → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jada (Nijeriya), 25 Nuwamba, 1946 (77 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Mutanen Fulani | ||
Harshen uwa | Adamaua-Fulfulde (en) | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Amina Titi Atiku Abubakar | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | customs officer (en) da ɗan siyasa | ||
Employers | Najeriya | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa |
Peoples Democratic Party All Progressives Congress | ||
atiku.org |
Farkon rayuwa
gyara sasheAtiku haifaffen jihar Adamawa ne.[7] An haifeshi a jahar Adamawa acikin garin Jada da ɗaya tilo awajen garba Abubakar mahaifinsa da mahaifiyarshi Aisha kande.https://newswirengr.com/2023/02/28/atiku-abubakar-biography-education-career-marriage-net-worth-achievements-and-controversy/
Siyasa
gyara sasheAtiku Abubakar yayi rashin nasarar samun zama shugaban kasar Najeriya a lokuta daban daban har sau bakwai. Daga shekarar 1993, 2007, 2011, 2015 , 2019 da Kuma 2023. A shekarar 1993, yayi takara a karkashin Social Democratic Party dan neman zama shugaban ƙasar amma ya sha kaye a wurin Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe. Ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Action Congress a Zaɓen Shugaban kasar Najeriya ta 2007 amma yayi rashin nasara da zuwa na uku a wurin Umaru Yar'Adua na jam'iyyar PDP da Muhammadu Buhari na ANPP. Ya nemi zama ɗan takarar shugabancin ƙasar a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party lokacin Zaɓen Shugaban kasar Najeriya ta 2011 nan ma yayi rashin nasara a hannun shugaba mai ci Goodluck Jonathan.[8] A shekara ta, 2014, Atiku ya koma jam'iyyar APC gabanin Zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya ta 2015 kuma ya nemi zama ɗan takarar jam'iyyar amma yayi rashin nasara a hannun Muhammadu Buhari. A shekarar, 2017, ya sake komawa jam'iyyar PDP a inda kuma ya zama ɗan takarar jam'iyyar a Zaben Shugaban kasar Najeriya ta 2019, sai dai har wayau ya sake rashin nasara a hannun shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.[9][10]. A shekarar, 2022 Atiku Abubakar ya bayyana sha'awarsa ta fitowa takarar shugaban kasa a Jam'iyyar PDP mai adawa inda zai kara da Bola Ahmed Tinubu na APC, da Peter Obi na Jam'iyyar Labour da Rabiu Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP da sauran Yan takara na kananan jam'iyyu. Bayan fafatawa mai zafi ta cikin gida da kuma ta sauran abokan karawa, hankula sun kasu gida daban-daban kuma da yawan jama'a sun kyautata zaton Atiku ne zai lashe Zaben. Daga cikin dalilan sa ran nasararsa har da rabuwar kanu a cikin ita jam'iyyar APC. Kari kan wannan, jama'a na cikin tsananin talauci da rashin tsaro a Birane da ƙauyuka. Wani abin damuwa shi ne yanda kwatsam gwamnati ta yi sauyin kudi wanda hakan ya jawo karancinsu a hannun mutane. Hatta da su mukarraban jam'iyyar APC sun zargi cewa an yi haka dan kassara tafiyar Tinubu. Atiku Abubakar ya nuna gamsuwar sa da wannan sauyin kuɗi. Bayan an yi zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu na shekarar, 2023, an kwashe kwanaki huɗu ana tattara sakamakon zaɓen kuma da asubahin wayuwar garin Laraba, shugaban hukumar zaben INEC ya bayyana Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Atiku Abubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria (entrepreneurs.ng)
- ↑ "Profile of Atiku Abubakar: From an only child of a father who opposed western education to a political guru". Nigeria Today. 2 October 2018. Archived from the original on 3 January 2019. Retrieved 3 January 2019.
- ↑ Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Abubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
- ↑ "Atiku Abubakar - the Nigerian operator who knows how to make money". BBC News (in Turanci). 2019-02-06. Retrieved 2020-09-11.
- ↑ https://leadership.ng/ex-president-obasanjo-visits-remi-tinubu-for-sallah-celebration/
- ↑ Podcast, N. L.; Giveaway, N. L. (2019-11-25). "Happy Birthday!! Atiku Abubakar Celebrates His 73rd Birthday (Drop Your Well Wishes) » Naijaloaded". Naijaloaded (in Turanci). Archived from the original on 2020-07-26. Retrieved 2020-05-29.
- ↑ "The Story of My Life by Atiku Abubakar". PM News Nigeria. 15 April 2019.
- ↑ Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Atiku AbAbubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
- ↑ "Atiku emerges PDP presidential candidate". The Punch (in Turanci). 7 October 2018. Retrieved 2019-04-19.
- ↑ "2023: Where Nigeria's President comes from, not important ― Atiku". Vanguard News (in Turanci). 2021-10-07. Retrieved 2022-02-22.
- ↑ https://punchng.com/topics/2023-elections Archived 2023-03-01 at the Wayback Machine