Kankiya
Kankiya na da dangantaka na musamman da masarautar katsina, a wajen kafa garin kankiya, tarihi ya nuna akwai wurare biyu, watau sabon garin kankiya da tsoho, a tsohon garin kankiya, akwai rijiyoyi guda takwas kuma akwai ramukan ɗiban farar ƙasa. A sabon birnin kankiya kuwa babu. An gina ganuwar kankiya a shekaru ɗari uku (300) da suka shuɗe[1].
Tarihi
gyara sasheHausawa suka fara zama a garin daga nan wasu fulani suka zauna a kudancin garin. Kanliya itace hedikwatar ƙaramar Hukumar ta, bayan zuwan turawa, sannan tana bisa hanya Katsina zuwa Kano, Nisan kimanin kilomita hamsin da shida (56) daga gari katsina zuwa kankiya[1]. Tarihi ya nuna cewa mutanen da suka fara kafa garin Kankiya mafarauta ne, kuma fatake ne a ƙarni na sha bakwai (17th century) sannan sun fito ne daga Arewa, a ƙalla mutanen dake zaune a garin sun kai dubu ishirin da shida (26,000). Gidajen sarautar kankiya sun haɗa da gidan Gunduma da gidan Haɓe (1861) gidan fulani da suka karɓa mulki wurin hausawa (1816)[2].
Cigaba
gyara sasheAn gina asibiti a garin a shekarar 1930, makarantan elementary a 1926[2], masallacin turawa a 1922[2], ɗakin shawara 1945, kurkuku 1956[3].
Biblio
gyara sasheTarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Tarihi, Hukumar Binciken. A shekarar (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 40. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 42. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 43. ISBN 978-2105-93-7