Siyasa
Siyasa hanya ce da mutane ke bi wajen rayuwa a hade, ko a tare, ko a kungiyance cikin manufa daya. Siyasa na nufin hada yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare duk da mabam-bantan ra'ayoyi, kabilu da addinai, a birane da kasashe. A manyan kashashe mutane da dama kan dauki dogon lokaci wajen tsayar da yarjejeniyar siyasa. Wadannan mutane su ake kira da Yan'siyasa. Yan-siyasa da kuma wadansu mutane kan hadu domin samar da Gwamnati da tafiyar da ita. Karatun tafiyar da gwamnati a jami'a ana kiranshi da Ilimin kimiyar siyasa (turanci Political Science, ko Political Studies).
![]() | |
---|---|
academic discipline (en) ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
group behaviour (en) ![]() ![]() |
Karatun ta |
political science (en) ![]() ![]() ![]() |
External data available at (en) ![]() | http://data.europa.eu/euodp/en/data/group/eurovoc_domain_100142 |
Gudanarwan |
ɗan siyasa da citizen (en) ![]() |
Tarihin maudu'i |
political history (en) ![]() ![]() |
Stack Exchange site (en) ![]() | https://politics.stackexchange.com |
A ma'anar ko yaushe Siyasa na nufin hanyar da kasashe ke bi domin aiwatar da mulki ko gwamnati, da kuma hanyar da gwamnatoci ke bi wajen aiwatar da dokoki. Ana kuma yin siyasa a wasu guraren kamar Kamfanoni, kungiyoyi, makarantu, masallatai da majami'u.