Daular Qajar
Qajar Iran (Farisawa ايران قاجارى Irân Qājāri) ana kuma kiranta da Qajar Farisa[1] (Farisawa فارس قاجارى Faris Qājāri), Daular Qajar (Farisawa شاهنشاهى قاجار Šāhanšāhi-ye Qājār), bisa hukuma Maɗaukakin Ƙasar Farisa (Farisawa دولت عَلیّهٔ ایران Dowlat-e 'Aliyye-ye Irân) kuma ana kiranta da Masarautu masu tsaro Iran (Farisawa ممالک محروسهٔ ایران Mamâlek-e Mahruse-ye Irân[2]) kasa ce ta Iran[3] wacce daular Qajar ta mulki daga 1789 zuwa 1925. Iyalan Qajar sun mamaye Iran gaba daya a shekara ta 1794, inda suka kori Lotf 'Ali Khan, Shah na karshe na daular Zand kuma suka sake tabbatar da ikon Iran akan manyan sassan Caucasus. A cikin 1796, Agha Mohammad Khan Qajar ya ƙwace Mashhad cikin sauƙi,[4] wanda ya kawo ƙarshen daular Afsharid. Iran ta hade kuma aka ayyana Agha Muhammad Khan Qajar shah na daular.[5]
Daular Qajar | |||||
---|---|---|---|---|---|
دولت عَلیّهٔ ایران (fa) Babbar kasar Iran ممالک محروسهٔ ایران (fa) Masarautu masu tsaro Iran | |||||
|
|||||
Taswirar Iran karkashin daular Qajar a karni na 19 | |||||
| |||||
Take |
(1873–1909) Salâm-e Shâh (Sallamar sarauta) (1909–1925) Salamati-ye Dowlat-e 'Aliyye-ye Iran (Gaisuwa ga babbar kasar Iran) | ||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Shah |
| ||||
Vazir-e A'zam |
| ||||
Firayam Minista |
| ||||
Babban birni | Tehran | ||||
Yawan mutane | |||||
Harshen gwamnati | Farisawa (wallafe-wallafen kotu / harshe, gudanarwa, al'adu, hukuma)Azerbaijani (harshen kotu da harshen uwa na gidan sarauta) | ||||
Addini | Shi'a | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Daular Zand Daular Afsharid Daular Durrani Khanatu na Kalat Masarautar Kartli-Kheti | ||||
Ƙirƙira | 1785 | ||||
Rushewa | 1925 | ||||
Ta biyo baya | Daular Pahlavi Daular Rasha Masarautar Afghanistan | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | Cikakken sarauta (1789–1906)tsarin mulki sarauta (1906–1925) | ||||
Gangar majalisa | Majalisar Shura ta kasa (1906–1925) | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi | Iranian toman (en) |
Daga baya juyin juya halin tsarin mulki ya faru. Bayan juyin mulkin da aka yi a zamanin mulkin Muzaffar al-Din Shah, sarki mai jiran gado Muhammad Ali Shah ya yi adawa da shi tare da rufe majalisar. Rikicin cikin gida da waje ya haifar da tashin hankali a kasar, kuma sarkin Qajar na karshe shi ne Ahmad Shah Qajar wanda aka hambarar da shi a shekara ta 1925 kuma Reza Pahlavi ya zama Shah na Iran.[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Qajar Persia.
- ↑ History of Persia.
- ↑ Abbas Amanat, The Pivot of the Universe: Nasir Al-Din Shah Qajar and the Iranian Monarchy, 1831–1896, I. B. Tauris, pp 2–3
- ↑ H. Scheel; Jaschke, Gerhard; H. Braun; Spuler, Bertold; T. Koszinowski; Bagley, Frank (1981).
- ↑ Iran : History.
- ↑ Qajar.