Jamhuriyar Musulunci
Jamhuriyar Musulunci suna ne da aka ba da nau'ikan gwamnatocin waɗansu ƙasashe. Waɗannan ƙasashe galibi suna da Musulunci a matsayin addinin ƙasa kuma ana gudanar da su da ƙa'idodin Shari'a, dokar musulunci. Dokokin da jihar ta yi ba za su saba wa Shari'a ba.
Jamhuriyar Musulunci | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | jamhuriya, Theocracy da Islamic state (en) |
Waɗannan jihohi suna kiran kansu Jamhuriyar Musulunci (jerin da ba na karewa ba)
- Iran (bayan an hambarar da Shah Mohammad Reza Pahlavi a 1979)
- Pakistan (Tun daga tsarin mulki na 1956, aka kafa ƙasar don samarwa da musulmai mazauna kasar Indiya mulkin mallaka, a 1947)
- Afghanistan (tun lokacin da aka hambarar da Taliban a 2001)
- Mauritania (tun daga 1958)
- Sudan
- Comoros (Jamhuriyar Musulunci ta Tarayyar)
- Gambiya (tun Disamba 2015)
Duk da irin wannan suna ƙasashen sun banbanta sosai a gwamnatocinsu da dokokinsu.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.