Rukunnan Musulunci Biyar (arkān al-Islām, larabci أركان الإسلام; ko arkān al-dīn, larabci أركان الدين, Rukunnan addini, Shika-shikan addini) abubuwa ne ko ayyuka waɗanda ginshiƙai ne, guda biyar a Musulunci, waɗanda wajibai ne akan kowane mai imani, kuma sune farkon ginshiƙin rayuwar Musulmi. Suna nan tattare a shahararren hadisin nan na mala'ika Jibril.[1][2][3][4]

Rukunnan Musulunci
obligation (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Ahkam (en) Fassara
Farawa 631
Amfani aqidah (en) Fassara da bauta a musulunci
Facet of (en) Fassara Usūl al-Dīn (en) Fassara da Foundations of the Islamic religion (en) Fassara
Sunan asali أَرْكَانُ الْإِسْلَامِ
Addini Musulunci
Suna saboda Submission (en) Fassara
Al'ada Arab world (en) Fassara da Duniyar Musulunci
Part of the series (en) Fassara Shari'a
Muhimmin darasi Fiƙihu
Mabiyi Huda (en) Fassara
Ta biyo baya iman (en) Fassara
Nau'in spiritual practice (en) Fassara da religious activity (en) Fassara
Mawallafi God in Islam (en) Fassara
Ƙasa da aka fara Hijaz
Harshen aiki ko suna Larabci
Mai kwatanta Jibril (en) Fassara da Muhammad
Commemorates (en) Fassara Muhammad prophecy (en) Fassara
Ma'aikaci Musulmi da Mukallaf (en) Fassara
Location of creation (en) Fassara Makkah da Madinah
Hashtag (mul) Fassara Five Pillars of Islam
Copyright status (en) Fassara public domain (en) Fassara

Shia, da Ahmadiyya, da Sunni dukkanin su sun yarda da muhimman bayani da ayyukan waɗannan abubuwan,[5][2] amma Shi'a basa ƙiran su da irin wannan sunan (see Ancillaries of the Faith, na Twelvers, da kuma Seven pillars of Ismailism). Sune suka haɗa rayuwar musulmi, sallarsa, taimakawa gajiyayyu, tsarkake kai daga zunubbai, da aikin hajji,[6][7] ga wanda yake da ikon zuwa.[8]

Shahada: (Imani)

gyara sashe

Shahada ita ce miƙa wuya da tabbatar da Imani da bada gaskiya dake yarda da cewar babu wani abun bauta idan ba (Allah) ba, kuma Annabi Muhammad Manzon Sa ne, Kalman shahada dai rukuni ne na farko daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar, wanda wajibi ne sosai mutum ya kiyaye ta , tana shigar da mutum cikin Musulunci in har ya furta , kuma ya kudur ce a zuciyar shi ,kuma yayi aiki da ma`anan abinda ya firta, kuma tana fitar da Mutum daga Musulunci idan ya saɓa ma`anar kalman ta hanyan yin saɓo ko shirka ko ya aikata wani aiki dake fitar da mutum daga Musulunci

Kalmar da kuma Ma`anarta

gyara sashe

Kalma itace kamar haka:- Na shaida babu abinda bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad Manzo n Allah ne.

 Ma`anarta shine ka yarda akan karan kanka ba tilasta ka akayi ba cewa Allah shi kaɗai zaka bautamawa , shine ka tsayar da Tauhidi guda uku Rububiyya da Uluhiyya da Asma`i wassifat , kuma  baza ka haɗa shi da kowa ba a gurin bauta , wato baza kayi Shirka ba ko Tsafi ko wani nauyin na hakan, kuma kaji ka yarda cewa Annabi Muhammad manzan Allah. Ma`ana ɗan aike ne daga Allah. Ma`ana duk abinda Annabi Muhammad yace zaka yarda kuma ka gasgata ,abinda yayi umurni dashi kuma ko yayi hani, zaka aika ta sau da kafa.  

.[9] Jawabi ne da yake a tsare, kuma ana furta shi ne da Larabci: lā ʾilāha ʾillā-llāhu muḥammadun rasūlu-llāh, (لَا إِلٰهَ إِلَّا الله مُحَمَّدٌ رَسُولُ الله) "Babu abun bautawa da gaskiya sai Allah (kuma) Annabi Muhammad Manzon Allah ne. Furta wannan jawabin nada muhimmanci sosai, Kafin mutum yazama Musulmi, ko ya dawo musulunci.[10]

Salah: (Sallah)

gyara sashe
 
Dattijon Musulmi lokacin Sallar Zuhur a Masallacin Jama

Sallah (ṣalāh) itace bautar musulmai, Sallah ta ƙunshi yin salloli biyar kamar yadda Sunnah tazo dasu; sunayensu akan lokutan Amfani: Fajr (Subhi), Dhuhr (rana), ʿAṣr (Yamma), Maghrib (Almuru), da kuma ʿIshāʾ (dare). Sallar Fajr ana gudanar da ita ne kafin fitowar(tasowar) rana, Dhuhr kuma ana yinta ne a tsakiyar rana, bayan rana tayi zawali, Asr kuma da yammaci ake yinta kafin faɗuwar rana, Maghrib da almuru bayan rana ta faɗi, sannan sai sallar Isha'i da ake yinta a cikin dare. Duk waɗannan salloli ana yinsu ne ta hanyar kallon Kaaba a Mecca daya samar da muhimmin ginshiƙi a cikin al'umman Musulmi. Musulmi sai sun wake jiki kafin yin Sallah; wannan wankin ake ƙira da wudu

Zakāh: (Zakkah)

gyara sashe

Zakkāh Zakka rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ana bayar da wani sashi ne na dukiyar mutum idan dukiyar ta kai nisabi.

Sawm: Azumi

gyara sashe

Azumi rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar , ana ƙin cin abinci ne da kuma ƙin shan abun sha tin daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana , haka za ayi tayi har sai anyi wata ɗaya na watan Ramadan tukunnan aka sauƙe nauyin farillan. [11] ref>Al Kur'ani 2:196</ref> .[12][13]


Hajj: Aikin Hajji

gyara sashe
 
Musulmai suna tafiya a ranar Arfa daga minna

Hajj itace ziyarar ibada dake faruwa a kowace watan musulunci na Dhu al-Hijjah zuwa Makkah. Kowani musulmi baligi dake da iko ya zama wajibi yayi aikin hajji a rayuwarsa koda sau ɗaya ne, Hajji rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ga wanda Allah ya bashi ikon zuwa ana yin aikin hajji ne kaɗai a makkah, kuma ba a son mutum ya tafi aikin hajji alhali akwai bashi akan shi ko iyalansa na cikin wani hali, ko kuma zasu shiga idan har ya tafi. .[14]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Pillars of Islam". Encyclopædia Britannica Online. Retrieved 2007-05-02.
  2. 2.0 2.1 "Pillars of Islam". Oxford Centre for Islamic Studies. United Kingdom: Oxford University. Archived from the original on 2009-02-11. Retrieved 2010-11-17.
  3. "Five Pillars". United Kingdom: Public Broadcasting Service (PBS). Retrieved 2010-11-17.
  4. "The Five Pillars of Islam". Canada: University of Calgary. Retrieved 2010-11-17.
  5. "The Five Pillars of Islam". United Kingdom: BBC. Retrieved 2010-11-17.
  6. Hooker, Richard (July 14, 1999). "arkan ad-din the five pillars of religion". United States: Washington State University. Archived from the original on 2010-12-03. Retrieved 2010-11-17. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)
  7. "Religions". The World Factbook. United States: Central Intelligence Agency. 2010. Archived from the original on 2018-12-20. Retrieved 2010-08-25.
  8. Hajj
  9. From the article on the Pillars of Islam in Oxford Islamic Studies Online[permanent dead link]
  10. Matthew S. Gordon and Martin Palmer, ''Islam'', Info base Publishing, 2009. Books.Google.fr. 2009. p. 87. ISBN 9781438117782. Retrieved 2012-08-26.
  11. Al Kur'ani 2:183–187
  12. Al Kur'ani 33:35
  13. Fasting, Encyclopedia of the Qur'an (2005)
  14. Farah (1994), p.145-147


[[Category:Kalma shahada]