Madinah Birni ne dake a yammacin Saudi Arabia nahiyar Asiya cikin tsakiyar yankin gabas ta tsakiya Baruch larabawa, ita dai wannan birni ya kafu ne tun dubban shekaru a baya tun a zamanin Annabawa. Hakika birnin Madinah garin Musulunci ne shine birnin manzon Allah Annabi Muhammad (s.a.w). Kafin zuwan Musulunci ana kiran birnin da suna Yathrib amma daga baya sai Annabi ya canjawa garin suna zuwa Madinah ko kuma Madinat Al-munawwarah a cikin birnin akwai babban masallaci wanda shine farkon Masallacin da Annabi ya gina a Madinah, wannan masallaci shine masallacin Quba

Globe icon.svg Madinah
Flag of Saudi Arabia.svg Saudi Arebiya
Madina.JPG
Administration
Sovereign stateSaudi Arebiya
Region of Saudi ArabiaAl Madinah Region (en) Fassara
babban birniMadinah
Official name المدينة المنورة
Original labels المدينة المنورة
Geography
Coordinates 24°28′00″N 39°36′00″E / 24.466666666667°N 39.6°E / 24.466666666667; 39.6Coordinates: 24°28′00″N 39°36′00″E / 24.466666666667°N 39.6°E / 24.466666666667; 39.6
Area 589 km²
Altitude 608 m
Demography
Population 1,180,770 inhabitants (2010)
Density 2,004.7 inhabitants/km²
Other information
Time Zone UTC+03:00 (en) Fassara
Sister cities Makkah
www.amana-md.gov.sa/
masallacin Annabi
Masallacin Annabi (s.a.w) dake birnin madinah


Fadin kasa

Birinin Madinah yana da fadin kasa kamar haka:

  • Fadin gari

589 km2 (227 sq mi)

  • Fadin babban birni

293 km2 (112 sq mi)

  • Maki mafi daukaka

608 m (1,995 ft)

  • kididdigar yawan mutane a shekarar (2010)

1,180,770

  • Density

2,000/km2 (5,200/sq mi)

Taswirar birnin Madinah
Wannan taswirar Birnin Madinah kenan.

Hakika birnin Madinah yanada matukar tasiri a Musulunci, shine garin Annabi Muhammad (s.a.w) bayan hijararsa daga birnin Makkah acikin garin yayi rayuwa har yakoma ga Allah, sannan kuma acikin birnin aka birne shi, acikin dakinsa inda yarasu, Wanda ayanzu nanne masallacinsa, Shi yasa duk Alhazan da sukaje Madinah to sai sun kai ziyara kabarinsa (s.a.w) da manyan sahabbansa.

Hotuna daga birnin MadinaGyara