Alwala da Larabci wudu, aiki ne na ibada da ake gabatar da shi a Musulunci gabanin yin Sallah, karatun alkur'ani da sauran su. Alwala na tsaftace mutum ne daga kananan zunubbai daya gabatar bai sani ba, shiyasa gabanin yin bauta, wanda ke kusantar da bawa ga ubangijinsa shi yasa ake gudanar da alwala don bawa ya samu tsarki da kwanciyar hankalin da zai gana da ubanginsa.

Wikidata.svgAlwala
Alwala
Ablucja-meczet.jpg
File:Wudu' ((الوضؤ)) Time.JPG
musulmi na yin alwala kafin sallah
butar alwala
alola

Yadda ake AlwalaGyara

idan ka samu ruwa mai kyau (Mai tsarki ) wanda yake tsarkakewa da kansa, bayan kayi tsarki wanda shari'a ta zo da shi wato a musulunce. Sai ka samu guri mai tsarki ka zauna, sai ka ajiye abun alwalanka a gefen dama idan budadde ne, idan kuma rufaffe ne sai ka ajjiye sa a bangarenka na hagu. Sai ka kudirta niyyarka a zuciyarka, bayan ka yi niyyar sai ka yi Bismillah (بسم الله) sai ka karkata abun alwalanka idan budadde ne ka zuba ruwan ka wanke hannuwanka sau uku bakin wuyan hannu zaka fara da na dama (×3) bayan ka wanke hannu sau uku daga nan zaka iya sa hannunka a cikin abun alwalan idan budadde ne, sai ka dibo ruwa ka kuskure baki sau uku (×3), Sai ka shaka ruwa sau uku ka fyace sau uku (×3) sai ka wanke fuska shi ma sau uku (×3) fadin fuska daga kunnen dama zuwa na hagu sai tsawo daga mafita gashin kai zuwa karshen haba, sai ka wanke hannu zuwa gwuiwar hannu sau uku (×3) da na dama zaka fara sannan na hagu, sai shafar kai da kuma dawowa da shafan kai, shafan tana farawa daga mafita gashin kai gaban goshi zuwa karshen keya, sai shafar kunnuwa biyu zaka sa manuni, yatsan kusa da babban yatsan hannu (sabbaba) cikin kunnuwa, sai babban yatsan hannu (Ibham) a bayan kunnuwa, sai ka wanke kafafuwanka biyu zuwa idon sawu, ana farawa da kafar dama sau uku (×3).

Addu'a da ake bayan an gama AlwalaGyara

(أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأشهد أن محمداً عبده ورسوله اللهم اجعلني من توابين واجعلني من المتطهرين .واجعلني من عبادك ل الصالحين Ash-hadu an lã ilãha illahu wahdahu lã sharika, wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu, Allahummaj'alni mina tawwabin waj'alni minal mutadahhirin waj'alni min ibadikassalihin . Daga nan ka gama Alwala sai sallah.[1] [2]

Farillan AlwalaGyara

Farilla alwala: 1. Niyyah.

2. Wanke fuska.

3. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu.

4. Shafar kai.

5. Wanke kafafuwa zuwa ido-sawu.

6. Cuccudawa da gaggautawa.

7. Ruwa mai tsarki.

Sunnonin AlwalaGyara

1. Wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa.

2. Kurkure baki.

3. Shaka ruwa.

4. fyacewa.

5. Dawowa da shafar kai.

6. Shafar kunnuwa. cikinta da bayanta

7. Sabunta ruwa dan shafar kunnuwa.

8. jeranta farillai.

Mustahabban AlwalaGyara

1. Yin bisimilla.

2. Yin asuwaki.

3. karawa a bisa wankewa na daya a fuska da hannaye.

4. Fara shafar kai daga goshi.

5. Jeranta sunnoni.

6. Karanta ruwa a kan gabbai.

7. Gabatar da wanke dama a kan hagu.

Wajabcin tsefe yatsun hannuGyara

Ya wajaba a tsefe yatsun hannaye, an so tsefe gashin gemu mara yawa a cikin alwala amma ban da mai duhu. Ya wajaba a tsefe shi a cikin wanka ko da mai yawa ne.

Gyaran alwalaGyara

Wanda ya manta farilla daga gabbansa na farilla,idan ya tuna a kusa sai ya wanke wannan farillar kuma ya sake wanke abinda yake bayanta, idan kuwa lokaci ya yi tsawo sai ya wanke ta ita kadai, sannan ya sake sallar da ya yi kafin ya wanke din.

Idan kuma ya bar sunna sai ya wanke ta ba zai sake salla ba. Wanda ya manta gurbin da bai sami ruwa sai ya wanke shi. Idan ya riga ya yi salla kafin wannnan sai ya sake Wanda ya tuna kurkure baki ko shaka ruwa bayan ya fara wanke fuska, ba zai dawo zuwa gare su ba har sai ya gama alwalarsa.

Allah Shi ne masani.

ManazartaGyara

  1. https://m.youtube.com/watch?v=2fFxdmn96kY
  2. "Farillan Alwala sunnoni Alwala". Retrieved 21 march 2021. Check date values in: |accessdate= (help)