Farilla
Farilla larabci-Fard (harshen-larabci|فرض) ko farīḍah (فريضة) a Musulunci aiki ne na ibadah daga Allah (Ubangiji). Kuma kalmar nan ana amfani da ita a harsuna da dama wanda ke da ma'anar daya data larabci, kamar a harsunan Persian, Pashto, Turkanci, da kuma harshen Urdu (da rubutu farz) amma ma'anar ba banbanci. Musulmai da suke bin umurnin dokokin ubangiji wurin yin biyayya ga ayyukan farilla ko umurni ana saka masu da lada wato da larabci hasanat, ajr ko thawab a duk lokacin da suka yi aiki mai kyau.
Farilla | |
---|---|
five decisions (en) da duty (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Ahkam (en) |
Facet of (en) | Musulunci |
Addini | Musulunci |
Gudanarwan | Musulmi |
Hannun riga da | haram (en) |
Farilla ko wājib (larabci|واجب) na daya daga cikin ire-iren hukunce hukunce guda biyar wanda a ciki ne fiqh suka karkasa nau'ikan ayyukan ibadah na kowane Musulmi. Fiqihun Hanafiyya dukda, sun banbanta tsakanin wajibi da farilla, wanda wajibi yake zama umurni da shi kuma farilla yake zama kawai wato abinda ake so.[1][2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ebrahim, Mufti (2002-04-28). "Albalagh.net". Albalagh.net. Retrieved 2019-01-29.
- ↑ Sunnipath.com Archived 2007-09-29 at the Wayback Machine