Shi'a
Shi'a (larabci شيعة Ko Shi'ah, Bangare, daga Shi'atu Ali ma'ana bangaren Sayyadina Aliyu) bangare ne a addinin Musulunci wanda mabiyansa suka yi amanna da cewa shi ne Halifa na farko bayan manzon Allah (s.a.w) wanda hakan ya sha babban da fahimtar Sunnah ko mabiya sunnah "Sunni Islam" wadanda suka yi imani da cewa ba Ali ne Halifa na farko ba. Suka ce Halifa na farko shi ne Sayyadina Abubakar (R. A). Hujjar Sunnah kuwa ita ce da yake Manzon Allah (s.a.w) bai nuna wani ba wanda za a bi bayansa sai suka yanke hukuncin yin Shura (wato kuri'a tsakanin al'umma) bayan Wafatin Annabi (s.a.w) kuma suka zabi Sayyadina Abubakar a matsayin Jagoran daular musulunci kuma jagoran Musulmai. Shi’a na ganin akasin haka, inda su kecewa Manzon Allah (saw) ya daga hannun Sayyidi Ali a Ranar Ghadeer kuma ya ce duk wanda ya ke masoyinsa ko majibincin lamarinsa to shi ma Ali ya kasance majibincin lamarinsa. [1]
Shi'a | |
---|---|
Classification | |
Sunan asali | الشِّيعَة |
Branches |
Ƴan Sha Biyu Zaidiyyah (en) ![]() Isma'ilism (en) ![]() Ghulat (en) ![]() |

Shi'a ita ce bangare na biyu a bangarorin Musulunci wanda ya fi yawan mabiya musamman a yankuna gabas ta tsakiya, bayan bangaren Sunna. A kididdigar da aka yi a shekarar 2009 'yan shi'a ne kaso 10-13% na al'umar musulman duniya. Shi'a 'Yan sha biyu ko (Ithna ashariyya) su ne suka fi yawa daga cikin 'yan shi'a inda suke da kaso 85% na mabiya mazhabin shi'a a kididdigar 2012.
Duk da haka akwai rabe-rabe masu yawa a shi'a, amma an fi sanin guda uku wato 'Yan sha biyu, Ismailyya da kuma Zaidiyya, amma ' yan sha biyu su ne mafiya yawa daga cikin bangarorin shi'a.
Bayanin kalmar Shi'aGyara
Kalmar Shia (Larabci: شيعة shīʻah /ˈʃiːʕa/) ma'ana mabiya ko bangare. Amma kalmaar shi'a anan tana nufin shīʻatu ʻAlī (شيعة علي /ˈʃiːʕatu ˈʕaliː/), ma'ana mabiya Sayyadina Aliyu ko yan bangaren Ali da Hausa ana iya kiransu a jam'i da Yan shi'a ko shi'awa, akidar kuma akan ce mata shi'anci.