Alqur'ani mai girma

Rubutun addinin musulunci na tsakiya
(an turo daga Al Kur'ani)

Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alkur'ani mai girma kamar yanda akasani, littafi ne mai tsarki wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga Annabin musulunci Muhammad (SAW). ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin akidar Musulunci, Kur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Annabi Muhammad (S.A.W), yana tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S A W) ne kuma Manzone na gaskiya.[1]

Alqur'ani mai girma
Asali
Shekarar ƙirƙira 631
Asalin suna القرآن‎
haɗawa a Makkah da Madinah
Characteristics
Genre (en) Fassara religious literature (en) Fassara da religious text (en) Fassara
Harshe Ingantaccen larabci
Kintato
Narrative location (en) Fassara Yankin Larabawa
masu karatun alqur'ani mai girma

Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Kur'ani (Madogararsa na Farko), tare da hadisai da ake ganin maganar Annabi Muhammad ne. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.

Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na dan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar hakkin dan adam na duniya, da 'yancin dan adam.[2]

Hotuna gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. dictionary.reference.com: koran
  2. https://www.iusinitinere.it/clash-between-sharia-law-and-human-rights-in-light-of-pace-resolution-2253-23827