Sunnah
Sunna Shi ne bangare mafi girma daga cikin bangarorin addinin Musulunci. Asalin sunan ya zo ne daga kalmar Sunnah, wato koyi da yin dukkan abun da Annabi Muhammad (S.A.W.) ya aikata, ko ya yi umarni da a aikata ko kuma aka aikata shi a gabansa amma bai yi hani ba. Bambanci tsakanin akidun Sunnah da kuma na Shi'a ya samo asali ne tun daga takaddama a kan wanda ya cancanci ya jagoranci al'umar Musulmi bayan wafatin Annabi (S.A.W.) wato Khalifanci. A bangaren fahimtar mabiya Sunnah sun ce, tunda yake Annabi (v) bai yi nuni ba da wani cewa shi za a bi to sai suka yanke hukuncin a bai wa surukinsa wato Sayyadina Abubakar ya zamo Khalifa na farko.
Sunnah | |
---|---|
![]() | |
Asali | |
Mawallafi | Muhammad |
Characteristics | |
Harshe | Larabci |
|
Amma a bangaren Mabiya Shi'a kuwa sai suka ce ai a ranar Ghadir Khumm Annabi (v) ya sanar da cewa ba wanda zai gaje shi sai dan'uwansa kuma sirikinsa wato Sayyadina Ali sun ce sabo da shi jininsa ne kuma surukinsa wato mijin 'yarsa Sayyida Fatima "Bint Nabiy".
Tun daga nan ne rikicin bangaren Sunnah da Shi'a ya samo asali.
A shekarar 2009 Musulmai mabiya Sunnah sun kai 87% zuwa 90%. Haka zalika Mabiya Bangaren Sunnah su ne bangare a Addini wanda suka fi ko wanne yawa a duniya bayan Katolika a addinin Kiristanci. Sanannu ne a sunan da suka yi fice da shi wato Ahlul Sunnah Wal Jama'a wato (al'umma mabiya sunnah).
Akidun mabiya SunnahGyara
Ga jerin akidojin Sunnah kamar Ha:
Shika-shikan Musulunci a wajen mabiya SunnahGyara
Shika-shikan Musulunci a wajen mabiya sunnah guda biyar ne sune.
Imani da Allah da Annabi Muhammada (S.A.W.)Gyara
Wato mutum ya furta kalmar SHahada kamar haka LA ILAHA ILALLAH MUHAMMAD RASULULLAH ma'ana mutum ya hakikance a ransa cewa BABU WANI ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH SANNAN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) BAWAN ALLAH NE KUMA MANZON ALLAH NE.
Tsai Da SallahGyara
Yin salloli guda biyar a kowacce rana watau ko wani yoni.
Da Azumi Watan RamadanGyara
Sai yin azumin watan Ramadana wato wata na tara a kalandar Musulunci.
Da Bada ZakkaGyara
Shine mutum ya cire wani adadi da shari'a ta fada na dukiyar sa ya bayar dashi ga mabukata Zakka saboda Allah.
==Da ziyartar Dakin Allah Ga Wanda Allah Yabawa Ikon Zuwa (Hajji)==
Idan Musulmi ya kasance yana da dukiyar da takai zai iya biyan ta wajen zuwa Saudiyyah kuma yana da karfin lafiya to Hajji ya hau kan sa.
Shika-shikan imani a wajen mabiya SunnahGyara
Shika-shikan Imani a makidar mabiya sunnah guda shida ne, gasu kamar haka.
Matsayin Hadisai a wajen mabiya SunnahGyara
Sanannun litattafan Hadisannan guda shida wato Kutub al-Sittah sune litattan hadisan da mabiya sunnah suka yi imani da gaskiyar hadisan dake cikin su Ga jerin su:
- Sahih al-Bukhari o na Muhammad al-Bukhari
- Sahih Muslim na Mislim ibn al-Hajjaj
- Sunan al-Sughra na Al-Nasa'i
- Sunan Abu Dawud na Abu Dawood
- Jami' at-Tirmidhi na Al-Tirmidhi
- Sunan Ibn Majah na Ibn Majah
Amma ba iyakar wadannan kadai bane litattafan da mabiya sunnah suka amince da gaskiyar hadisan dake cikin su ba, akwai wadansu litattafan da dama wadanda suka hada da:
- Musannaf na Abd al-Razzaq na ‘Abd ar-Razzaq as-San‘ani
- Musnad na Ahmad ibn Hanbal
- Mustadrak na Al Haakim
- Muwatta na Imam Malik
- Sahih Ibn Hibbaan
- Sahih Ibn Khuzaymah of Ibn Khuzaymah
- Sunan al-Darimi na Al-Darimi
Iyalan gidan Annabi (S.A.W.) a mahangar SunnahGyara
Su ne DUKKAN DANGIN Manzon Allah (SAW) wadanda sadaka ta haramta garesu, da kuma MATANSA da ZURIYYARSA. Allah ya yarda da su gaba daya. Sabanin AkidunShi'a ko Rafidanci Wadanda suke cewa Iyakacin Nana Fatima da Imamuna Aliyu da suran zurriyar su,sune kadai Iyalan gidan Manzon Allah (S.A.W.). Wannan gurguwar fahimta ce a mahangar Mabiya Sunnah.
Ahlus Sunnah sun yi ITTIFAQI akan WAJABCIN Son Ahlul Baiti, da kuma HARAMCIN Cutar dasu,ko Munana musu,da magana ko aiki.
Sahabbai a mahangar mabiya SunnahGyara
Sahabbai Sune dukkan mutanen da suka ga Annabi (S.A.W.) sanna Kuma suka bayar da gaskiya da shi, a lokacin da yake da rai. Wadannan mutane suna da matsayi mai girma tare da samun girmamawa daga wajen mabiya akidar sunnah.
Mabiya Sunnah suna yin cikakkiyar soyayya da biyayya ga sahabbai ne sakamakon wadansu ayiyin Alkur'ani inda Allah da kansa yake yabon su,kamar haka:
Kuma magabatan farko na Muhajirai da Ansarai da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su kuma sun yarda da shi,kuma ya yi musu tattalin gidajen aljanna, qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne rabo mai girma.
- Suratut Taubah: 100
A wannan aya mutane sun kasu kashi uku. Muhajirai da Ansarai da wadanda suka bi su da kyautatawa ba da zagi ba.
Sai kuma aya ta gaba:
Muhammad manzon Allah ne. Kuma wadanda da ke tare da shimasu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, ka na ganinsu suna masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu, da yardarsa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujuda. Wannan ita ce siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu a cikin Linjila ita ce, kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya qarfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan qafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah ya yi alqawali ga waxanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan qwarai daga cikinsu da gafara da lada mai girma
- Suratul Fathi, Aya ta 29
Sahabbai goma wadanda akayi masu albishir da shiga Aljannah tun suna duniya. Manzon Allah (S.A.W.) yana da Sahabbai 120,4000. Duk da cewa dukkan wadannan Sahabbai 'yan Aljanna ne to amma akwai wadanda akayi musu bishara da Aljanna tun suna da rai.
Akwai guda goma wannan Manzon Allah (S.A.W.) ya fada a hadisi cewa an yi musu bishara da gidan Aljanna, wato ASHARATUL MUBASHSHIRUN. Wannan Sahabbai sune:
- Abubakar Saddik (R.T.A.)
- Umar Bin Khaddab (R.T.A.)
- Usman Bin Affan (R.T.A.)
- Aliyu Bin Abi Dalib (R.T.A.)
- Dhalha Ibn Ubaidullah (R.T.A.)
- Zubair Ibnul Awwam (R.T.A.)
- Abdurrahman Bin Auf (R.T.A.)
- Sa'ad Bin Wakkas (R.T.A.)
- Sa'id Bin Zaid Bin Amr (R.T.A.)
- Abu Ubaidah Bin Jarrah (R.T.A.)
Allah Madaukin Sarki ya bamu albarkacin wadandan bayi nasa..