Fulani

Wata ƙabila ce a najeriya wacce take a Afrika ta yamma
(an turo daga Fulfulde)

Fulani ko Fulata (tilo: Bafulatani ko Bafillace) Mutane ne da ke a Yamma Maso Arewacin Afrika tun a tsawon lokaci. Mafi shaharar sana'ar Fulani shi ne kiwon dabbobi da kuma saida nono, kuma suna tatsan nonon dabbobinsu domin sayarwa, Fulani wasu mutane ne da ke da kyakkyawar fahimta, da zamantakewar sukan zauna da kowane kabilu lafiya kuma har su kulla aure a tsakaninsu. Kididdiga ta nuna cewa akwai fulani akalla miliyan talatin da biyar a Najeriya.

Fulani

Yankuna masu yawan jama'a
Sudan, Sudan ta Kudu, Burkina Faso, Laberiya, Gambiya, Muritaniya, Najeriya, Nijar, Cadi, Mali, Kameru, Ghana, Saliyo, Togo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Ivory Coast, Guinea-Bissau, Benin, Gine, Habasha da Eritrea
tsohuwar (Nayejo) fulani dauke da kwarya nono
wata matar Fulani tare da yaran ta sun kewaye ta, tana wanke-wanke
fulani da shanun su
Fulani suna tashi sun dora yaran su akan jaki

Harshe gyara sashe

Harshe ko yaren da kuma Fulani suke magana da shi sunan sa Fulfulde. Haka ake kiran sa a kasashen Najeriya, Nijar, Sudan da Kamaru, amma a tushen inda suka fito, watau kamar 'kasashen Senegal, Mauritaniya,Gini, da sauransu ana kiran harshen da Pulaar' ko Fula.

 

ASALIN KALMAR FULANI gyara sashe

Da fari dai, masanin ya fada cewar tabbataccen tarihi shi ne wanda ya zo a Alkur'ani da Hadisai, amma duk wani abu wanda ba shi ba kan iya zamowa gurbatacce, don haka bai doru a kan cewa wajibin duk abinda ya faɗa shi ne na gaskiya ba.


A cewar sa asalin sunan Fulani shi ne Tuta (Futa Toro), kuma suna cikin tsoffin kabilun duniya ne. Shi sunan Futa din sun samo shi ne daga kakansu/uban su da ake kira Futa, kuma shi jika ne ga Annabi Nuhu. Ta wajensa aka samar da Samudawa da Adawa, don haka fadin Ta Ala a Alkurani (IRAMA ZA TUL IMAAD) da kabilar su yake, domin an samu cewa an taba kiran su da suna Iramawa.


Daga bisanin saboda yawaitar su ga yake-yake, sai aka rinka kiransu da suna Fatah, ma'ana Jarumai. Sannu a hankali kuma aka koma ambaton su da suna Futa.


Yanayin zaman su a wurare kuwa shi ne silar sauyawar sunayen su, ta yadda ake kiran wasu Futa Toro, ma'ana Futawa mazaunan Toro, da Futa Masina, Futa Jallo, Futa Falgo da sauran su


A cewar masanin, shi wannan sunan na FULANI, ya samo asali ne a Yammacin Afirka, sanda suka hadu da kabilar MANDINKA wajen zama, wadanda su ma kusan Fulani ne a halaye da dabi'u.


Malam Ahmad ya tafi a kan cewa Fulani kabilar farko ce da suka soma zaman Afirka, kuma su ne suka zo da addini Yammacin Afirka, amma fa addinin Yahudanci. Shi kuwa kowa ya sani addini ne na jinsi, ba na kowa da kowa ba.


Don haka idan Fulanin sun tara 'ya'yansu, su kan sanar musu da cewa 'Ana Hulbe (Fulbe) Allah'. Ma'ana mu masu tsoron Allah ne, kada kuyi abinda Mandinkawa abokan zaman mu suke aikatawa. Daga nan sai mandinkawa masu zuwa ganin su suka rinka kiransu da suna Fulah, kafin daga bisani sunan ya rinka sauyawa zuwa Fullata, da Fulbe.


ASALIN BAFILLATANI MAHANGA TA DAYA


Malam Ahmad ya sanar mana da cewa Bafillatani ya samu ne daga Annabi Nuhu A S.


Asalin zuriyarsa kuma a yankin durun Sinin take da zama. A nan ne har Annabi Musa A.S ya riske su a zamaninsa lokacin da aka saukar masa da Attaurah. A lokacin suna masu bautar shanu, don haka, sai ya kira iya kabilar sa Bani Israila zuwa bautar Allah makaɗaici.


Shi ya sa sai Bani Isra'ila suka yi kwadayin a sanya musu abin bauta kamar yadda Futawa suke yi, har kuma Musa Samiri ya shagaltar da su tare da sanya musu dan maraki a matsayin abin bautar Annabi Musa A .S.


Sai daga baya Annabin Allah Musa ya gane lamarin, sannan ya kira shugabansu mai suna Tori ya karbi addini, shi ne har aka yi bikin karbar sa ranar Asabar a jikin dutsen duri Sina. Fulani na kiran bikin 'Larki'. Har kuma sukan ce "RaduTori Sinin", watau ga Inda Tori ya musulunta wajen nuni da duri Sinin.


A wannan zamanin, sai kabilar Futah ta kasu. Wasu suka karbi addinin Annabi Musa bisa biyayya da shugaban su Tori, wasu kuma suka bijere, inda suka yi Hijira zuwa Afirka ta Kudu, daga jikin su kabilun Chusi da ake kira Totsi yanzu suka fita, da sauran kabilun da suka mamaye yankunan.


ASALIN BAFILLATANI MAHANGA TA BIYU


Aka ce asalin Fulani tare da Yahudawa suke da zama. Don haka kusancin su ke sanyawa ake kiransu da sunan Yahudawa. Kuma su mayaka ne mara sa tsoro, wadanda ba sa rabo da makami, sannan suna matukar daukaka ranar Asabar sama da sauran ranaku saboda tarayyar su da Yahudawa. Sannu a hankali suka famtsama yankin Afirka ta Yamma.


ASALIN FULANI MAHANGA TA UKU


Wannan mahangar kuma ta nuna cewa Fulani tsatso ne daga zuriyar Annabi Ayyuba A.S..

Aka ce a lokacin da ya zama dattijo yana wa'azi a gefen tekun Indiya, sai aka ba shi wata mace aure wadda ba ta son sa. Don hakan idan dare ya yi sai ta guje masa zuwa bayan daki, a can kuma sai shedan ya rinka zuwar mata yana tarawa da ita. A haka har ta samu rabon yaro namiji wanda baya magana da kowa.


Aka yi magana a kan yadda ta samu wannan yaro dube da rashin tarayyar ta da maigidanta, amma Annabi Nuhu ya ce a kyale ta a matsayin matarsa, daga bisani hakan ya cigaba da faruwa har ta sake haifar yarinya mace.


Don haka wadannan mace da namijin da suka girma su ne suka fara amfani da yaren su sabo na Fulatanci.


Tarihi gyara sashe

Arziki gyara sashe

Wasanni gyara sashe

Fannin tsarotsaro gyara sashe

Kimiya da Fasaha gyara sashe

Sifiri gyara sashe

Sifirin Jirgin Sama gyara sashe

Sifirin Jirgin Kasa gyara sashe

Al'adu gyara sashe

Mutane gyara sashe

DURI

Abinci gyara sashe

Daga cikin muhimman abincin Fulani akwai Fura.

Tufafi gyara sashe

Ilimi gyara sashe

Addinai gyara sashe

Musulunci gyara sashe

Hotuna gyara sashe

Maza gyara sashe

Mata gyara sashe

Manazarta gyara sashe