Abubakar Tafawa Balewa

Sir Abubakar Tafawa Balewa KBE, An haifi Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekara ta 1912.[1]

Simpleicons Interface user-outline.svg Abubakar Tafawa Balewa
Balewa.jpg
1. Firayim Minista na Nigeria

1 Oktoba 1960 - 15 ga Janairu, 1966
← no value - no value →
Rayuwa
Haihuwa Bauchi, 1912
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Lagos, 15 ga Janairu, 1966
Makwanci Bauchi
Yanayin mutuwa kisan kai
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya da marubuci
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Northern People's Congress (en) Fassara
kabarin abubakar tafawa balewa kenan

Yayi karatu a makarantar horas da malamai ta Katsina daga (1928 zuwa 1933), sannan ya zamo malami, kuma shugaban makarantar Middle School dake bauchi. Sannan

Yayi karatu a makarantar horas da malamai ta London daga (1945 zuwa 1946), inda ya samu shaidar malanta.

A lokacin yakin duniya na biyu ya nuna sha'awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na Bauchi Discussion Circle.

Sannan daga bisani ya shiga siyasar malamai inda aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kungiyar malaman Arewa.

A shekara ta 1952 ya zamo ministan ayyuka na Najeriya, sannan ya kuma zamo ministan sufuri a shekara ta 1954, sannan ya zamo jagoran jam'iyyar NPC a [majalisar wakilai]] ta kasa.

Ya zamo Firayim Ministan farko na Najeriya bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar ta 1960.

A shekarar ta 1966, wasu sojoji suka yi kokarin juyin mulki inda anan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe marigayin Sir Abubakar Tafawa Balewa. [2][3]

Farkon Rayuwarsa da AikiGyara

Abubakar Tafawa Balewa an haife shi a karshen shekara ta 1912 a garin Bauchi. Mahaifinsa Yakubu Dan Zala mutumin Gere ne[4] mahaifiyarsa Fatima Inna itama tanada dangi daga Gere da kuma Fulani.[4]

 
Abubakar Tabawa Balewa
 
Tabawa Balewa
 
Mariyagi Abubakar Tabawa Balewa

Yafara karatunsa a makarantar allo a garin Bauchi kuma kamar sauran abokansa na wannan lokacin, shima yaje makarantar Kwalejin Barewa domin ci gaba da karatunsa da gama warsa ne yasami sakamakon zama malamin makaranta. Ya dawo garin Bauchi yafara karantarwa a Bauchi Middle School. A shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da hudu (1944), tare da wasu tsirarun malamai 'yan'arewa aka zabe su suyi karatu a kasar waje na shekara daya a jami'ar Landon (University of London)'s (Institute of Education) fannin karatun malunta, wanda ayanzu itace bangaren University College London. Bayan dawo warsa Nigeria, yazama jami'i mai binciken makarantun na gwamnatin turawan mulkin mallaka, bayan nanne yatsunduma cikin siyasa, A shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da shida (1946), an zabeshi zuwa majalisar arewacin Najeriya, sannan yaje ta Lagos a alif dubu daya da dari tara da arba'in da bakwai(1947). A matsayin sa na Dan majalisa, yazamanto mai Neman 'yancin Nijeriya tareda Alhaji Ahmadu Bello, wanda shine keda sarautar Sardaunan Sokoto, ya kirkiri jam'iyyar yan arewa (NPC).

ManazartaGyara

  1. https://www.bbc.com/hausa/mobile/news/2010/09/100922_tafawabalewa_history
  2. https://www.britannica.com/biography/Abubakar-Tafawa-Balewa
  3. https://www.bbc.com/hausa/multimedia/2016/01/160115_tafawa_balewa_picture
  4. 4.0 4.1 Kperogi, Farooq (22 Jan 2016). "Gere: Sir Abubakar Tafawa Balewa's Real Ethnic Group". Daily Trust. Retrieved September 5, 2016.