Samuel Akintola
Samfuri:Infobox Prime Minister
Samuel Akintola | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ogbomosho, 6 ga Yuli, 1910 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Mutuwa | Ibadan, 15 ga Janairu, 1966 |
Yanayin mutuwa | kisan kai |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, aristocrat (en) , orator (en) da Lauya |
Imani | |
Addini | Kirista |
Jam'iyar siyasa | Nigeria National Democratic Party |
Cif Samuel Ladoke Akintola, wanda aka sani da SLA (rayuwarsa ta kasance daga Yuli 6, shekarar 1910 zuwa Janairu 15, shekarar 1966), ɗan siyasa ne a Najeriya, lauya, dattijon ƙasa kuma mai gabatar da fatawa wanda Kuma aka haifa a Ogbomosho, na nan yankin yammacin kasar. Baya ga kasancewarsa daya daga cikin iyayen da suka kafa Najeriya ta zamani, an kuma daga martabar shi zuwa matsayin Oloye Aare Ona Kakanfo XIII na Yarbawa.
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Akintola ne a garin Ogbomosho ga dangin Akintola Akinbola da na Akanke, mahaifinsa dan kasuwa ne kuma ya fito ne daga ahalin 'yan kasuwa. [1] A lokacin da yake ƙarami, iyayensa sun yi kaura inda suka koma Minna inda ya ɗan samu damar samun ilimi daga makarantar Church Missionary Society dake cikin Birni. A shekarar 1922, ya dawo Ogbomosho ya zauna tare da kakansa sannan daga baya ya halarci makarantar kwana ta Baptist kafin ya ci gaba zuwa Kwalejin Baptist a shekarar 1925. [1] Ya koyar a makarantar Baptist Academy daga shekarar 1930 zuwa 1942 kuma daga nan yayi aiki na ɗan lokaci tare da Kamfanin Railway na Najeriya . A wannan lokacin, ya saba da Cif H.O. Davies, lauya kuma dan siyasa kuma ya shiga kungiyar Matasan Najeriya inda ya taimakawa Ikoli kuma ya goyi bayan wanda zai wakilci Lagos a majalisar dokoki kan takarar Oba Samuel Akisanya , wanda Azikiwe ya goyi bayansa. [1]
Aiki
gyara sasheAkintola ya shiga cikin ma'aikatan Jaridar Labarai ta Daily kuma ba da daɗewa ba ya zama edita a shekarar 1943 tare da goyon bayan Cif Akinola Maja, wanda ke da hannun jari a kamfanin, ya maye gurbin Ernest Ikoli a matsayin edita. Akintola shi ma ya kafa Jaridar Iroyin Yoruba, wata jarida ce da ake rubutawa da yaren Yarbanci. A shekarar 1945, ya yi adawa da yajin aikin gama-gari wanda jam'iyyar Azikiwe ta NCNC da Michael Imoudu suka jagoranta, hakan ya haifar da rashin amincewar ‘yan siyasa irin su Cif Anthony Enahoro . [1] A shekarar 1946, ya samu gurbin karatu a Burtaniya don yin karatu a Burtaniya kuma ya kammala karatun shari'a a shekarar 1950. Ya fara aikin lauya yana aiki a matsayin lauya kan lamuran ƙasa da matsalolin mutane. A shekarar 1952, ya kulla kawance da Cif Chris Ogunbanjo, Cif Bode Thomas da Michael Odesanya. [1]
Harkar siyasa
gyara sasheMutuwa
gyara sasheAn kashe Akintola a Ibadan, babban birnin yankin Yammaci, a ranar juyin mulkin soja na farko a Najeriya na 15 ga Janairu 1966 — wanda ya kawo karshen Jamhuriya ta Farko . [2] Wanda kuma aka fi sani da "Young Majors Coup" ko "coup of the January boys", juyin mulkin ya haifar da kisan manyan 'yan siyasa da yawa, galibi mambobin jam'iyyar Majalisar Wakilan Arewa (NPC). [3]
Rayuwar Iyali
gyara sasheAkintola ya auri Faderera Akintola wadda ta haifa masa 'ya'ya biyar, biyu daga ciki (Yomi Akintola da Dr. Abimbola Akintola) duk sun taɓa rike mukaman ministocin kudi a Jamhuriya ta Uku a Najeriya . Yomi Akintola ya kuma sake yin aiki a matsayin Jakadan Najeriya a Hungary kuma surukar Samuel Akintola, Dupe Akintola, ta kasance Babbar Kwamishinar Najeriya a Jamaica.
Manazarta
gyara sasheMedia related to Samuel Akintola at Wikimedia Commons</img>