Ahmadu Bello

Ɗan siyasar Najeriya

Sir Ahmadu Bello (An haife shi ranar 12 ga watan Yuni, shekara ta 1910) a karamar hukumar Rada da ke a jihar Sakkwato.[1] Sardauna shine tsohon Firimiyan Arewacin Najeriya kuma ya rike sarautar Sardauna a jihar Sakkwato. A shekarar 1949, ya sami zuwa majalisar dokoki ta yankin Arewa, yana kuma daga cikin mutum ukku da aka zaba acikin kungiyar da ta rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar.[2]Sardauna mutum ne dake da mahimmanci sosai ga mutanen arewacin Najeriya, dama fadin kasar baki daya, saboda irin ayyukan cigaba daya kirkiro a yankin arewa harma da kudancin kasar gaba daya. Kamar Jami'ar Ahmadu Bello, Gidan Rediyo dake Jihar Kaduna, da sauransu. Duk da cewa Sardaunan Sokoto Sarauta ce tashi a Jihar Sokoto, amma sunan ya zama kamar wani inkiya a gareshi inda ya shahara wajen amsa shi a ciki da wajen Najeriya.

Ahmadu Bello
Rayuwa
Haihuwa Rabbah (en) Fassara, 12 ga Yuni, 1910
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Kaduna, 15 ga Janairu, 1966
Yanayin mutuwa kisan kai
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Northern People's Congress (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu bello
Ahmadu bello sardauna tare da wasu mutane
hoton sardauna lokacin da yake kaddamar da dakin taro a jihar oyo
sir ahmadu bello
Estate Katsina steta Ahmedu Bello Sardaunan sokoto

Farkon Rayuwarsa

gyara sashe

Ahmadu Bello Sardauna, an haife shi ne a garin Raba, shekara ta alif dubu daya da dari tara da tara (1909), a Gidan Malam Ibrahim Bello. Mahaifinsa shi ne Sarkin Raba.[3] kuma zuri'ar Usman Dan Fodio ne, kuma tattaba kunnen Sultan Muhammad Bello kuma jikan Sultan Atiku na Raba. Yayi makarantar Sokoto Provincial School da kuma Katsina Training College. Lokacin karatun sa an sansa da Ahmadu Raba.[3] Ya kammala karatun sa ne a shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da daya (1931), Sannan yazama babban Malamin harshen turanci a Sokoto Middle School.

 
Ahmadu bello sardaunan sokoto da sa'adu alanamu da kuma wani mutumi

A shekarar alif dari tara da talatin da hudu (1934), an nada Ahmadu Bello hakimin garin Raba daga Sultan Hassan dan Mu'azu, inda yagaji dan uwansa. A shekarar alif dari tara da talatin da takwas (1938), an masa karin girma a matsayin Shugaban Gusau dake jihar Zamfara a yau, kuma yazama mabiyi a masarautar Sultan's council. A shekarar alif ɗari tara da talatin da takwas (1938), yana da shekara 28, yayi kokarin zama sarkin sokoto amma bai samu nasara ba, yasha Kaye a hannun Sir Siddiq Abubakar II wanda yayi mulki na tsawon shekaru hamsin (50), har sai sanda yarasu a alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas(1988). Sai sabon Sarkin yayi maza ya naɗa Sir Ahmadu Bello da Sardaunan Sokoto, sarautan girmamawa kuma yakaisa ga matsayin Sokoto Native Authority Council. Wadannan muka man ne suka kai shi har ya zama babban mai bawa sultan shawara akan harkokin siyasa. Daga bisani, aka bashi ikon duba gundumomi arba'in (47) daga alif dubu daya da dari tara da arba'in da hudu (1944), ya dawo fadar maimartaba Sultan danyin aiki a matsayin babban mai kula da jaha akan al-amura na gargajiya (Chief Secretary of the State Native Administration).

A kuma shekarun alif dubu daya da dari tara da arba'in (1940s), sai ya shiga cikin Jam'iyyar Mutanen Arewa wanda daga baya takoma NPC a shekarar 1951. A shekarar 1948, yasamu tallafin karatu daga Gwamnati zuwa kasar Ingila Dan yin karatun Local Government Administration wanda ya kara masa karin ilimi da fahimtar gwamnati.

 
Sardauna na gaisawa da Queen Elizabeth ta biyu

. Bayan dawowarsa daga Britain, an zabe shi ya wakilci yankin Sokoto a regional House of Assembly. A matsayinsa na member of the assembly, ya kasance dakare wajen kare

hakkin arewacin Najeriya da kuma hakin kan wakilan yankin wadanda suka fito daga manyan masarautun arewa, wato Kano, Masarautar Borno da Sokoto. An zabeshi da wasu a matsayin member of a committee wadanda sukayi Richards Constitution kuma yaje general conference a Ibadan. Aikin sa a assembly da kuma gun tsarin constitution drafting committee ya janyo masa yarda da kauna a arewa, hakane yasa aka zabe shi da yayi mulki a karkashin Jam'iyyar Mutanen Arewa.[3] A zabukan da aka gudanar na farko a arewacin Najeriya a 1952, Sir Ahmadu Bello yasamu nasarar zuwa a Northern House of Assembly, kuma yazama member of the regional executive council as minister of works. Ahmadu Bello ya rike ministan ayyuka, dana Local Government, da minister of Community Development in the Northern Region of Nigeria. A shekarar 1954, Bello yazama Premier na farko a Northern Nigeria. A kuma shekara ta 1959 a zabukan yancin kai, Ahmadu Bello ya jagoranci jam'iyar NPC har ya samu nasara da yawan kujeru a majalisar kasa. NPCn da Bello ke jagoranta ta kulla kawance da jam'iyar Dr. Nnamdi Azikiwe NCNC (National Council of Nigeria and the Cameroons) to form Nigeria's first indigenous federal government which led to independence from Britain. In forming the 1960 independence federal government of the Nigeria, Bello a matsayinsa na shugaban NPC, ya zaɓi yaci gaba da zama Premier na Arewacin Nijeriya sannan ya bayar da matsayi.

Yadda aka kashe Sardauna

gyara sashe

Kafin ya tafi Umara a Janairun shekarar 1966, sai da ya kai ziyara zuwa Sokoto domin yiwa yan' uwa sallama. Wadanda suke tare da shi duk sun kula da alamomin sarewa da duniya a tattare da shi. An ce kafin kisan sa, har wasika ya karba na bankado asirin kisan sa daga shugaban Misra, Jamal Abdul Nasser, amma sardauna yayi burus,yace mutum baya tsallake kaddarar sa. Duk da dai cewa gwamnan Yamma Dr. Awolowo ya zo ya samu Sardauna akan kishin-kishin din cewa sojoji suna shirin yi musu juyin mulki, amma Sardauna ya ki basu damar daukan wani mataki. A ranar 15 ga watan Janairu, wajen karfe 10 na dare, Major Nzeogu Kaduna da yaransa suka shiga gidan firemiya suka sake shi yana lazimi, suka harbe shi da bindiga har lahira.Hakazalika har ɗaya daga cikin matan sa suka kashe. Bayan nan suka sanya wa gidan wuta. Sheikh Abubakar Gumi ne ya shirya jana'izar, sannan ya sallaci firemiya washegari. Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai minista Ibrahim Musa Gashash, Usman Kafin Baki, Turai Aliyu,Dr. Dikko da manyan ma'aikatan gwamnati. An binne shi wajen karfe 12-1 na ranar 16 ga wata. Duk wadanda suka kitsa juyin mulkin dukkan su kananan sojojin inyamurai ne. Daga dalilan wadanda suka kashe shi har da cewa suna zargin sa da raba kan kasa da maida hankali kan Arewacin Najeriya. Bayan wannan bai ma yarda da kasar Isra'ila ba da take jaririya a lokacin.

  • Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila., Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
  • ·        Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710
  • The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366
  • ·        Sardauna media coverage, 1950-1966 : His Excellency Sir Ahmadu Bello ... Sardauna of Sokoto, late Premier of Northern NigeriaISBN978-978-49000-2-7OCLC696110889
  • ·        Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (2009). Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto, late Premier of Northern Nigeria : selected speeches and quotes, 1953-1966. Kaduna, Nigeria: Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation. ISBN 978-978-49000-1-0. OCLC 696220895.
  • . Paden J.N (1986). Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto: Values and Leadership in Nigeria. Hudahuda publishing company, Zaria.

Manazarta

gyara sashe
  1. Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila., Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle.p.1 ISBN 978-34637-2-1.
  2. http://www.dw-world.de/dw/article/0,,2846635,00.html
  3. 3.0 3.1 3.2 cite news |last=Savage |first=Babatunde |date=1959-03-16 |title=Profile of a Fearless Leader |url= |newspaper=Daily Times |location=Lagos |access-date=