Pidgin na Najeriya

Yaran turanci ne na pigin

Wannan harshen Turanci ne na cikin gida wanda kusan yawancin 'yan Nijeriya ke amfani da shi, musamman mutanen kudancin kasan. Ana kiran yaren da pijin ko broken english. Akan yi amfani da harshen a matsayin pijin, ingausa, ko kuma a salon fasahar sarrafa harshe wanda ake amfani da su dangane da yanayin mu'amala.[2] Akwai littafi da aka yi don koyar da harshen pidgin kuma ya samu karbuwa matuka a gurin mutane.[3][4]

Pidgin na Najeriya
Pidgin na Najeriya
pidgin
'Yan asalin magana
47,500,000
harshen asali: 4,700,000 (2020)
Baƙaƙen boko
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 pcm
Glottolog nige1257[1]
Pidgin na Najeriya
nogerian pidgin

Ba a Najeriya kadai ake amfani da wannan harshen na Pidjin ba, har da kasashen ketare kamar Benin, Ghana, Cameroon da sauransu.[5]

Misalin ya kake? a turance wato how are you? zai zama how you dey? a harshen pidjin.[6]

Ana amfani da harshen pidjin a sassa daban daban na Najeriya, amma har yanzun kuma ba'a zartar da shi a matsayin 'yantaccen harshe ba. Harshen pidjin yana bada damar cudanya tsakanin harsuna daban daban na Najeriya[7] kuma ana amfani da ita wajen magana a sassa daban daban na kasar.

Bambance-bambance

gyara sashe

Yawancin harsuna daban daban (250) na Najeriya na iya amfani da yaren pidjin sai dai akwai bambanci wasu kalmomi dangane da wurare. Misali, Yarbawa kanyi amfani da kalmar Ṣebi da Abi a yayin magana da harshen, wanda akan sanya su a farko ko karshen jimla. Misali, "Zaka zo ko?" a turance "You are coming, right?", a pdjin Ṣebi you dey come? ko kuma You dey come abi?

Wani misalin shi ne yadda inyamurai ke amfani da kalmar "Nna" wanda ake amfani da shi a farkon jimla don jaddada muhimmancin magana. Akwai wata kalma da inyamurai ke yawan amfani da it's wajen magana kamar "Una" wanda aka aro daga kalmar inyamuranci "Unu" wanda ke nufin "abu masu kama da juna" ko mutane biyu, misali "Una dey mad" ma'ana "baku da hankali".

Har wayau, salon sarrafa harshen pidjin ya bambanta a wurare daban daban. Yaren pidjin ya hada da asalin wurare da suka hada da Warri; Sapele; Umuahia; Benin City; Port Harcourt; Lagos (musamman Ajegunle); da kuma Onitsha.

Mafi yawanci an fi amfani da yaren pidjin a yankin Niger Delta inda mutane da yawa ke amfani da shi a matsayin yarensu na farko. Akwai zancen da ya tabbatar da cewa a Najeriya aka fara amfani da harshen pidjin wanda daga bisani ya ketara zuwa kasashen yakin Afurka ta yamma.

Dangantakan Pidjin da sauran yaruka

gyara sashe

Kamanceceniya da Ingausar Carrebiya

gyara sashe

Pidjin din Najeriya tare da sauran pidjin na kasashen nahiyar Afurka na da dangantaka da ingausar da ake amfani da ita a yankin Carreniya. Salon furucin harshen na da bambanci da na Carrebiya amma idan da za'a rubuta shi ko a fada a hankali za'a ga cewa akwai kamanceceniya tsakaninsu.

Dangantaka da yaren Portugal

gyara sashe

Har ila yau akwai kalmomin da ake amfani da su a Pidjin wanda sun samo asali ne daga yaren Portugal wanda zuka zauna a yakunan Edo da Delta musamman lokacin cinikayyar bayi a yankin. Misali, kalmar "sabi" wanda ke nufin "iyawa" ya samo asali ne daga harshen Portugal "saber" wanda ke da ma'ana iri daya. Kamar ace "za ka/ki iya" (a turance "can you do it?") a pidjin kuma "you sabi do am"?. Dangane da labarin ka'idojin pidjin, kalmar sabir ta samo asali ne daga kalmar aro na harshen Portugal. Har wayau kalmar pikin wanda ke nufin yaro karami ya samo asali ne daga yaren Portugal wanda ke nufin "pequeno" da kuma "pequenino" wanda suke nufin "karami" ko kuma "karamin yaro" a jere.

Turancin Najeriya

gyara sashe

Kamar dai ingausar yankunan Carrebiya, ana amfani da pidjin ne wajen harkokin yau da kullum amma ba'a harkokin gwamnati ba. Haka zalika wannan yaren pidjin bai da matsayi a gwamnatance a Najeriya. Ana koyan turanci ne a makarantu na boko.[8]

Kara bita

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Pidgin na Najeriya". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
  2. "Faraclas, Nicholas C., Nigerian Pidgin, Descriptive Grammar, 1996, Introduction.
  3. "IFRA Nigeria – Naija Languej Akedemi". www.ifra-nigeria.org. Retrieved 2019-02-09.
  4. Esizimetor, D. O. (2009). What Orthography for Naijá? Paper delivered at the Conference on Naijá organised by the Institut Français de Recherche en Afrique (IFRA), July 07-10, 2009, University of Ibadan Conference Centre.
  5. Fitimi, Prince; Ojitobome, Afinotan. "THE EFFECT OF THE NIGERIAN PIDGIN ENGLISH ON THE ACADEMIC PERFORMANCE OF UNIVERSITY STUDENTS IN NIGERIA. ACASE STUDY OF NATIONAL OPEN UNIVERSITY OF NIGERIA STUDENTS IN BENIN STUDY CENTRE".
  6. "Faraclas, Nicholas G. (2020-06-30). Nigerian Pidgin. Routledge. p. 25. ISBN 0-203-19280-X.
  7. "Language Contact Manchester". languagecontact.humanities.manchester.ac.uk. Retrieved 2018-07-17.
  8. "Florence Agbo, Ogechi; Plag, Ingo (2020-12-11). "The Relationship of Nigerian English and Nigerian Pidgin in Nigeria: Evidence from Copula Constructions in Ice-Nigeria". Journal of Language Contact. 13 (2): 351–388. doi:10.1163/19552629-bja10023. ISSN 1877-1491.