Umar

Umar (/ˈuːmɑːr/), Wasu na rubutawa haka Omar (Larabci: عمر بن الخطاب)‎ Umar ibn al-Khaṭṭāb "Umar, dan Al-Khattab"; Yayi rayuwa daga shekara ta 584 CE zuwa 3 ga watan Nuwambar shekarar 644 CE. An haife shi a shekara ta 584 a garin Makkah, Saudiya. Yarasu a watan Nuwamba 3, shekarar 644 (Shekarunsa, 59–60) a garin Madina, Saudiya. An birne shi tare da Manzon Allah da Sayyidina Abubakar, a gidan Manzon Allah wanda a yanzu shine masallacin Manzon dake Madina. Yakasance daya daga cikin matukar karfi da daukakan Halifofin musulunci. Yana daga manyan Sahabban Manzon Allah, Muhammad tsira da amince su tabbata agare shi. Yagaji Shugaba Abubakar a Halifanci daga (632–634) 23 August 634. Kwararre fakihi ne, wanda yayi suna akan tsoran Allah da tabbatar da adalci, hakan tasa ake masa lakabi da Al-Farooq (Mai babbancewa tsakanin Karya da Gaskiya). Ana kiransa da Umar I ( wato Umar na daya) sanadiyar samun wani shugaba daya biyo bayansa daga jikokinsa shima mai adalci, wato Umar II.

Umar ibn Al-Khattab عمر بن الخطاب Al-Faruq Sarkin Muminai Amir al-Mu'minin, Halifofi shiryaryu, Babban Sahabi, Shahidi Mai babbancewa tsakanin Gaskiya da Karya, Daya daga Goman da akayi wa umurnin shiga aljannah, Yayi Halifanci daga 23 Augusta shekara ta 634 CE zuwa ga watan 3 Nuwamban shekara ta 644 CE. Yagaji Sayyidina Abu Bakr, sai kuma Uthman ibn Affan yagaje shi. Matansa sune: Zaynab bint Madhun, Umm Kulthum bint Jarwal, Qurayba bint Abi Umayya, Jamila bint Thabit, Atiqa bint Zayd, Umm Hakim bint al-Harith, Umm Kulthum bint Abu Bakr. Yayansa; Abdullah ibn Umar, Abdulrahman ibn Umar, Zayd ibn Umar, Ubaydallah ibn Umar, Az-Zubayr "Abu Shahmah", ibn Bakkar Asim ibn Umar, Abdulrahman (Abu'l-Mujabbar) ibn Umar, Iyaad ibn Umar, Abdulrahman ibn Umar, Zayd ibn Umar, Yayansa mata; Hafsa bint Umar, Fatima bint Umar, Ruqayya bint Umar, Zaynab bint Umar,

Dan kabilar Kurayshawa (Banu Adi) Mahaifinsa shine; Khattab ibn Nufayl Mahaifiyarsa itace; Hantamah binti Hisham.