Uthman ibn Affan (larabci: عثمان بن عفان‎), Usman, Osman, Uthman. ya kasan ce yayi rayuwa ne daga shekara ta (577 zuwa 17ga watan Yunin shekara ta 656). An kuma haife shi ne a shekara ta 577 (45 BH) wanda ke garin ɗaif, dake a Saudiya, ya kuma rasu ne a shekara ta 17 ga watan wanda tayi dai dai da (17 Dhūl Al-Qa‘dah 35 AH) (shekara ta 656 ) (ya rayu tsawon shekaru 77) an birne shi ne a garin Madinah, wanda ake kira Jannatu al-Baqi dake Madinah. Yakasance sirikin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata agareshi, wanda ya aura masa 'ya 'ya biyu daga cikin 'ya'yan sa, shine ake kiransa da suna (zunnuraini) wato me ma'abocin Haske 2, Halifan Musulunci na Uku, Ɗaya daga cikin Halifofi shiryayyu, Ɗaya daga cikin Sahabbai Goma 10 waɗanda akaiwa bushara da gidan Aljannah tin a nan gidan Duniya, ɗan zuri'ar Banu Umayyah daga ƙabilar Kurayshawa.[1] Sanda Sayyidina Umar yarasu da shekaru 59/60, ʿUthmān, yana da shekaru 64/65 a duniya sai ya gaji Umar bin Khaddab bayan rasuwarsa. Uthman ibn Affan Yayi Halifanci daga 6 ga watan Nuwamba shekara ta 644 zuwa 17 ga watan Yuni shekara ta 656.

Simpleicons Interface user-outline.svg Usman Ibn Affan
Balami - Tarikhnama - the election of 'Othman as the caliphate of Medina (cropped).jpg
Khalifofi shiryayyu

5 Nuwamba, 644 - 17 ga Yuni, 656 (Gregorian)
Sayyadina Umar - Sayyadina Aliyu
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 574
ƙasa Hijaz
Khulafa'hur-Rashidun
Mutuwa Madinah, 17 ga Yuni, 656 (Gregorian)
Makwanci Al-Baqi'
Madinah
Yanayin mutuwa kisan kai (blunt trauma (en) Fassara)
Killed by Abd Allah bin Saba'
Ƴan uwa
Mahaifi Affan ibn Abi al-'As
Mahaifiya Urwa bint Kariz
Abokiyar zama Umm Amr Bandage Jundub (en) Fassara
Ramlya bint Shayba (en) Fassara
Umm al'-Banin bint Ayni (en) Fassara
Fatima Bint Al-Waleed (en) Fassara
Q68678851 Fassara
Ummu Kulthum  (624 -
Na'ila bint al-Farafisa (en) Fassara  (641 -  17 ga Yuni, 656)
Rukayyah  (unknown value -  624)
Yara
Ahali Umm Kulthum bint Uqba (en) Fassara, Walid ibn Uqba (en) Fassara, Khàlid ibn Uqba ibn Abi-Muayt (en) Fassara, Aminah bint Affan (en) Fassara da Umara ibn Uqba (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Ƙarƙashin jagorancin Uthman, Khalifancin Rashidun ya faɗaɗa zuwa Fars ( Iran ta yau) a cikin 650, da wasu yankuna na Khorāsān ( Afganistan a yau) a shekara ta 651. An fara cin Armeniya a cikin 640s.[2] Haka kuma mulkinsa ya yi ta fama da zanga-zanga da tashe -tashen hankula wanda a karshe ya kai ga tayar da makamai da kuma kashe shi .

Usman bin Affan yarasu ne sanadiyar farmaki da aka afka masa. An samu wasu yan tada kayar baya game da addinin Musulunci tare da kin shugabancin sa. Wanda suka afka masa alhali yana karatun alqurni. Tarihi ya nuna an kashe shi ne akan zalunci wanda hakan yasa aka haura katangar gidansa sannan aka kashe shi. Ali Ibn Abi-Talib ne ya gaje shi bayan rasuwarsa. Matayensa; "Ummu 'Amr; Asma'u bintu Abi Jahal, Ruqayyah bintu Muhammad, Ummu Kulthum bint Muhammad, Fakhitah bintu Ghazwan_ Ummu al-Banin bintu Uyayna, Fatima bintu al-Walid Daughter of Khalid ibn Asid Umm 'Amr Umm Najm bint Jundub Ramla bint Shayba, Bunana Na'ila bint al-Furafisa, Zaynab bintu Hayyan. Bakurayshe (Banu Umayya) Mahainfinsa: Affan ibnu Abi al-'As Mahaifiyarsa: Arwa bintu Kurayz.

Uthman ya auri yar Manzon Allah Ruqayyah, kuma bayan ta rasune, Manzon Allah yasake aura masa yar'sa Umm Kulthum. Dukkaninsu sun kasance manyan ya'yan Manzon Allah Muhammad kuma yayye ga Fatimah yar Manzon Allah matar Aliyu bin Abi Dalib, saboda ya aura yayan Manzon Allah biyu ne yasa ake kiransa da Dhū al-Nurayn ("Wanda ya mallaki Haske biyu").

ManazartaGyara

  1. Tabatabai, Sayyid M. H. (1987). The Qur'an in Islam : its impact and influence on the life of muslims. Zahra Publ. ISBN 978-0710302663.
  2. Ochsenweld, William; Fisher, Sydney Nettleton (2004). The Middle East: A History (6th ed.). New York: McGraw Hill. ISBN 978-0-07-244233-5.

tarihin usman Ibn affhan khalifa na uku bayan wafati monzon allah saw an zabeshi bayan wafati sayyidina Umar r.t bayan ya rasu sai aka zabi sayyidina Ali Ibn abu dalib a tarihin sayyidina usman mutun ne mai imani mai tsoran allah Wanda malanmai sunyi fadi cewa yasamu kyautar aljanna har sau hudu sannan mutun ne mai tsananin kunya allah kabamu ikon fadin gaskiya kuma katsareni daga sharrin mai sharrin dan albarkacin sayidil anbiya ina kaunar rasulallahi da ahali da sahabai nai baki daya da duk Wanda yabi tafarkine ya allah ka tabbatar da mu akan addinin ka na musulumci damu da iyayanmu da kannan mu da iyalan mu da duk Wanda yake musulmi da kuma wadanda basuyi imani ba allah kashiresu albarkacin masu imani daga naku Hassan Salifou ango kunkuzutt