Khula'hur-Rashidun (a Larabci, Khilafa-al-Raahidah آلخلافة ألراشدة) Sune Kalifofin farko guda hudu ko kuma magada na jagorancin Daular Musulunci tun bayan Wafatin fiyayye halitta Annabi Muhammad (s.a.w) a shekara ta 632M wato 11H. Khulafa'ar-Raahidun sune sukayi shugabancin Daular Musulunci daga 632-661M. Musulmai mabiya Sunnah wato Sunni Islam ne ke kiran su da sunan Khulafa'hur-Rashidun, amma a bangaren mabiya Shi'a wannan kalmar bata amfani domin kuwa sun hakikance da Kalifofin ukun farko kafin Sayyadina Ali sunyi kwace ne, kuma basa ganin su da girmamawa.

Khulafa'hur-Rashidun
الخلافة الراشدة (ar)

Wuri

Babban birni Madinah da Kufa
Yawan mutane
Harshen gwamnati Larabci
Addini Musulunci
Labarin ƙasa
Bangare na Khalifofi
Bayanan tarihi
Mabiyi Medina community (en) Fassara
Wanda ya samar Sayyadina Abubakar
Ƙirƙira ga Yuni, 632
Rushewa 28 ga Yuli, 661
Ta biyo baya Khalifancin Umayyawa
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati elective monarchy (en) Fassara da Theocracy
• Khalifofi shiryayyu Sayyadina Abubakar (6 ga Yuni, 632)
Ikonomi
Kuɗi dinar (en) Fassara
Tambari

Khulafa'hur-Rashidun sunyi kalifanci ne na shekara 25

Taswirar daular Khulafa'hur-Rashidun

Bayan Wafati Annbi (s.a.w) ne sahabban sa suka fara tattaunawa game da ko wanene zai gaje shi wajen jagorancin musulmai a yayinda sukuma iyalan gidansa suna can suna shirya Janazar sa. Sayyadina Umar da Abu Ubaidullah ibn al-jarrah suka nuna mubaya'ar su ga Sayyadina Abubakar.

Tarihin Khulafa'hur-Rashidun

gyara sashe
 
thumb taswirar daular kalifofi hudu mai baiyana fadadar daular tun daga kalifan farko

Bayan Wafatin Annabi Muhammad (s.a.w) a shekarar 632 miladiyya, sai Mutanen Madina (Ansar) suka fara tattaunawa akan wanene zai gaji Kalifancin Musulmi a tsakanin su. Sai suka zabi Sayyadina Abubakar ya zama kalifa na farko na Musulunci. Daganan sai shi kalifan na farko yaci gaba da jan ragamar Musulmai da aiwatar da al'amuran Musulmi da yada addini tsakanin kasashen makabta na larawa da sauran kabilu. Tsarin Kalifanci baya nufin sarauta, tun daga Kalifan farko har na karshe basa daukar kansu a matsayin sarakuna. Domin Kalifanci na nufin Jagorancin Annabta (ma'ana jaogoranci na al'amuran musulmi kwatankwacin na annabta).

Kalifofin da suka biyo bayan kalifan farko sune, Sayyadina Umar, wato kalifa na biyu, sai Sayyadina Usman, kalifa na Uku, sai Sayyadina Aliyu, kalifa na hudu. Daganan kuma kalifanci ya kare sai sarauta.