Babban Masallacin Makkah (da larabci; ٱلْـمَـسْـجِـد ٱلْـحَـرَام a furucci; al-Masjid al-Ḥarām a ilimance; Masallaci mai Tsarki, da turanci; The Sacred Mosque)[1]) shine masallacin daya zagaye Kaaba dake birnin Mecca, Saudiya. Wuri ne na ziyara domin aikin hajji, wanda kowane Musulmi dole ya aikata shi, karanci sau daya a rayuwarsa idan yana da ikon zuwa, wanda aikin yahada da kewaye dakin Kaaba dake a cikin masallacin. Kuma nan muhimmin wurin yin ‘Umrah, karamin aikin hajji da akeyi a kowane lokaci a cikin shekara. Babban masallacin yahada da wasu mahimman wurare, wadanda suka hada da, Baƙin Dutse, Rijiyar ZamZam, wurin tsayuwar annabi Ibrahim, da duwatsun Safa da Marwa.[2] A bude Masallacin yake, akowane lokaci da yanayi.

Madina Building, Hyderabad.jpg
Masallacin Harami lokacin aikin Hajji na shekarar 2009

Babban Masallacin harami shine masallaci mafi girma a duniya, kuma anmasa gyararraki da fadada shi a lokuta daban-daban a shekaru.[3] Ta wuce lokuta da dama ƙarƙashin kulawar Halifofi daban-daban, sultans da sarakuna, kuma ayanzu babban masallacin na ƙarƙashin kulawar Sarkin Saudi Arabia wanda shine Custodian of the Two Holy Mosques.[4] Tana nan ne a gaban Abraj Al Bait, mafi tsayin ginin agogo a duniya,[5] aikin gininsa dake cike da cece-kuce akan rushed wuraren tarihi na farkon musulunci da gwamnatin Saudiya tayi.[6]

Wannan ƙasida guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


AnazarciGyara

  1. Denny, Frederick M. (9 August 1990). Kieckhefer, Richard; Bond, George D. (eds.). Sainthood: Its Manifestations in World Religions. University of California Press. p. 69.
  2. Al Kur'ani 3:97 (Translated by Yusuf Ali)
  3. https://www.bbc.com/news/world-middle-east-34231620
  4. "Is Saudi Arabia Ready for Moderate Islam? - Latest Gulf News". www.fairobserver.com (in Turanci).
  5. "As we prepare to fall back, here are seven great clocks of the world". Los Angeles Times (in Turanci). 2017-10-29. ISSN 0458-3035.
  6. Carla Power. "Saudi Arabia Bulldozes Over Its Heritage". Time.