Alqur'ani mai girma
Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an) ko kuma Alkur'ani mai girma kamar yadda musulmi suka fada, littafi ne mai tsarki wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga Annabin musulunci Muhammad (SAW). ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin akidar Musulunci, Kur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Annabi Muhammadu, yana tabbatar da cewa Muhammadu Annabi ne kuma Manzone na gaskiya.[1]


Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Kur'ani (Madogararsa na Farko), tare da hadisai da ake ganin maganar Annabi Muhammadu ne. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.
Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na dan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar hakkin dan adam na duniya, da 'yancin dan adam.[2]
Hotuna Gyara
-
Mushafin Ibn al-Bawwab.
-
surah daga cikin surorin alkur'ani, al-Kahf
-
Mushafin al-qurani tun karni na 7 shekara dari bayan wafatin Annabi Muhammad SAW a Birmingham kasar Ingila
-
mushaf din Imam Ali RA
-
Bugun Qur'ani a 1907
-
Rubutun qurani a warsh da turanci
-
Dakin alkuranai a Meseum din al-Quran a Melaka.
Manazarta Gyara
- Quran Word by Word // QuranAcademy.org
- Translation of the Meanings of the Quran into Hausa
- ↑ dictionary.reference.com: koran
- ↑ https://www.iusinitinere.it/clash-between-sharia-law-and-human-rights-in-light-of-pace-resolution-2253-23827