Tarihi
Tarihi wane muhimmin abu ne, wanda yake ba wa al'umma damar sanin wane abu da ya wuce a baya hausawa kan ce "Kunne ya girmi kaka." Wato yaro da aka haifa kwanannan zai iya sanin abin da kakansa ma bai sani ba ko kuma ba a haifeshi shi ba sanda abun ya faru. Idan muka duba wannan karin magana za mu ga cewa tabbas tarihi ya na da amfani tunda zai ba ka damar sanin wani abin da ya faru shekara da shekaru.dalinlin tarihi ne kadai ake sani abubuwan da suka a da chan baya.
![]() | |
---|---|
set (en) ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
research object (en) ![]() ![]() |
Karatun ta |
study of history (en) ![]() |
Stack Exchange site (en) ![]() | https://history.stackexchange.com |
Classification of Instructional Programs code (en) ![]() | 54, 54.01, 54.0101 da 54.0199 |
Facet of (en) ![]() |
past (en) ![]() |
Dukkan wata al'umma da ba ta damu da tarihi ba, to ba shakka ta na cikin matsala saboda ba za su san su waye ba.
An san tarihi ta hanyoyi da dama kamar haka:
- Rubutu
- Furta sa baki
- Amfani da kayan zamami
A cikin waɗannan hanyoyi ingantacciya kuma tabbatacciya ita ce hanyar rubutawa, larabawa su na cewa ما كتب قررا وما حفظ فررا Wato rubutacce tabbatacce ne haddatacce kam ƴatacce ne. Idan ba a rubuta abu ba ta tabbas wata rana ana iya neman sa a rasa.