Muhammad bn Ali ( larabci : محمد بن علي الباقر), wanda aka fi sani da al-Baqir ( wanda ya bude ilimi ) (677-733) shi ne limami na biyar daga cikin limaman shia. [1] Shi ne dan Ali bin Husayn ko Zayn al-Abidin kuma imam na farko wanda ya fito daga jikokin Muhammad da Hasan bn Ali da Husayn bn Ali . Musulmin Sunni da Shia suna matukar girmama shi saboda shugabancinsa, iliminsa da kuma ilimin addinin Musulunci a matsayin masanin shari'a a Madina . Bayan wafatin Ali bn Husayn (Imami na huxu), mafi yawan ‘yan Shi’ar sun yarda da dansa al-Baqir a matsayin imami na gaba; wasu daga cikinsu suka ce, wani dan imam Zayd bn Ali shi ne imami na gaba, kuma ya zama ana kiran sa da Zaidiyyah . [2]

Al-Baqir
5. Limamai Sha Biyu

712 - 733
Ali ibn Husayn - Jafar ibn Muhammad
Rayuwa
Haihuwa Madinah, 8 Mayu 677
ƙasa Umayyad Caliphate (en) Fassara
Harshen uwa Larabci
Mutuwa Madinah, 26 ga Janairu, 733
Makwanci Al-Baqi'
Yanayin mutuwa  (dafi)
Killed by Hisham ibn Abd al-Malik (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Ali ibn Husayn
Mahaifiya Fatimah bint al-Hasan
Abokiyar zama Farwah bint al-Qasim (en) Fassara
Yara
Ahali Zayd ibn Ali (en) Fassara, Husain bin Ali bin Husain (en) Fassara da Abdullah bin Ali bin Al Hussein (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Harsuna Larabci
Malamai Ali ibn Husayn
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a Liman da muhaddith (en) Fassara
Imani
Addini Ƴan Sha Biyu

Manazarta gyara sashe

  1. A Brief History of The Fourteen Infallibles. Qum: Ansariyan Publications. 2004. p.117.
  2. See Ibn Khallikan, trans. de Slane, Vol. III, p. 274.