Pandogari

Gari ne a jihar Neja, Najeriya

Pandogari garine ko kuma ƙauye ne dake a ƙaramar hukumar Rafi, Kagara a jihar Neja, Najeriya. Kagara itace shelkwatar karamar hukumar Rafi. Tsakanin pandogari da babban birnin jihar Neja wato Minna kusan 156.7km ne garin Pandogari yana akan hanyar Birnin Gwari, wadda ta zarce har Kaduna haka kuma garin Pandogari yana akan hanyar Lagos. Pandogari tana karkashin masarautar Hakimin kwangwama wadda take a cikin garin har iyau ita Kuma masarautar pandogari tana karkashin masarautar Kagara Alhaji Idris Aliyu shine Hakimin Pandogari, shine sarki na 3 da suka mulki garin Pandogari kuma shine na 2 kasancewar ya sauka ya kuma sake zamowa hakimin Pandogari. Pandogari tanada yaruka 3 wadanda kusan sune daga kaje zaka ci karo dasu; akwai Hausawa, sai Fulani da kuma Ɓurawa duk da cewa wasu na ganin asalin garin Pandogari ɓurawa ne suka kafa shi sai dai kuma yanzu zallar su suna a kauyukan Pandogari ne suma Fulani suna a kauyukan garin a cikin kwaryar garin hausawa ne zalla sai dan sauran kabilun da ba'a rasa ba irin Yarbawa, Igbo, Kamukawa, Pongu da dai sauransu. A shekarar 2016 an samu wani rikicin Addini wanda ya haddasa rasa rayukan mutane kusan 4 ciki hada wani matashi dan Makaranta a cikin garin Pandogari, Kusan ana cewa wannan matashin shine wanda ya sabbaba rikicin tunda shine ya yada kalaman batanci ga Manzon Tsira da Rahama (S A W) a kafar sada zumunta ta Facebook, shi kuma matashin Kirista ne shiyasa rikicin yake tsakanin Musulmai da kiristoci rikicin yasa anyi kone-konen shaguna da wuraren bauta. A karshe gwamnatin jihar Neja a karkashin Abubakar Sani Bello ta aiko da jami'an tsaro aka kwantar da tarzoma.[1][2][3][4]

Pandogari
Wuri
Map
 10°24′00″N 6°25′00″E / 10.4°N 6.4167°E / 10.4; 6.4167

Sanannun Mutane a Pandogari

gyara sashe
  • Imam Habib Lawal (Babban Limamin Yan Izala, Pandogari)
  • Alhaji Idris Aliyu (Hakimin Kwangoma)
  • Alhaji Ado Tela (Dan Kasuwa)
  • Alhaji Aminu Wayo (Dan Kasuwa)
  • Alhaji Salisu mai wake (Dan Kasuwa)
  • Muhammad Bagobiri (Malamin Yan Darikar Tijaniyyah)
  • Late Alhaji Aliyu Ahmad Bafillace Ringa (Malamin Addinin Musulunci kuma jagoran Fulani)
     
    Mariganyi Alhaji Aliyu Ahmad Bafillace
  • Alhaji Abubakar Jibo Garba (Madakin Kagara)
  • Late Alhaji Sama'ila Hayin Sarki (Manomi)
  • Alhaji Zubairu Isma'il (Dan Majalisar dake wakiltar karamar hukumar Rafi a Majalisar Dokokin Jihar Neja)
  • Mamman Dogo (Dan siyasa kuma kansilan pandogari)

Ƙauyuka/garuruwan dake kusa da Pandogari

gyara sashe
  • Gidan awane
  • Gidan buhari
  • Gidan damao
  • Gidan kurao
  • Gidan madawakin tugulbi
  • Gidan maigari boka
  • Gidan maikarfi
  • Gidan maizaji
  • Gidan sarkin uguru
  • Gidan sarkin Uran chiki
  • Gidan shabagu
  • Gidan tanko
  • Gidan tetige
  • Gidan ushiba
  • Gidan wusheynu

Sanannun Wurare a Pandogari

gyara sashe
  • Government Day Secondary School Pandogari
  • Mamman Kwantagora Technical College Pandogari
  • Central Primary School Pandogari
  •  
    Shedikwatar yaren ura
    Kyareke Primary Health Care Pandogari

Tafiyar/Nisa tsakanin Pandogari da wasu birane a Najeriya

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Niger State Governor Wades Into Pandogari Crisis". channelstv.com. 1 June 2016. Retrieved 13 December 2021.
  2. "4 killed, church, others burnt as religious violence breaks out in Niger at Pandogari". vanguardngr.com. 31 May 2016. Retrieved 13 December 2021.
  3. Dipo, Laleye (2 June 2016). "Niger Govt Sets up Investigative Panel on Religious Crisis". thisdaylive.com. Retrieved 13 December 2021.
  4. Salisu Abubakar, Hassana (24 July 2019). "LABARAI Niger:yan bindinga sun sace wasu yan kasuwa 18 a garin Pandogari". freedomradionig.com. Retrieved 13 December 2021.