Fezbuk
An dai kafa shafin sadarwa ta Facebook ne a watan fabairun shekara ta 2004 a ƙasar Amirka. Kuma wasu matasa uku wato Zuckerberg da Chris Hughes da kuma Moskovitz ne suka ƙirkiro shafin a wannan shekarar. Wanda dai akace ya jagoranci kafa shafin na Facebook tsakanin matasan dai shine Mark Moskovitz ɗan shekaru 23 a duniya dake karatun Sanin halayan ɗan Adam wato Psychology, a lokacin da yake ɗalibta a jami'ar Harvard dake ƙasar ta Amirka domin anfanin ɗaliban jami'ar.
URL (en) | https://www.facebook.com, https://facebookwkhpilnemxj7asaniu7vnjjbiltxjqhye3mhbshg7kx5tfyd.onion da https://m.facebook.com |
---|---|
Eponym (en) | face book (en) |
Gajeren suna | FB |
Iri | social networking service (en) , yanar gizo, Dandalin sada zumunta, user-generated content platform (en) , online community (en) da very large online platform (en) |
Language (en) | Turanci, Traditional Chinese (en) , Simplified Chinese (en) da Harshen Japan |
Programming language (en) | PHP (mul) |
Mai-iko | Meta Platforms (mul) |
Maƙirƙiri | Mark Zuckerberg |
Service entry (en) | 4 ga Faburairu, 2004 |
Kyauta ta samu | 'Verschlossene Auster' award (en) |
Alexa rank (en) |
3 (7 Nuwamba, 2017) 3 (20 Nuwamba, 2017) 5 (2 Oktoba 2019) 3 (16 Mayu 2019) 3 (23 Oktoba 2017) |
Official blog URL (en) | https://about.facebook.com/news |
FacebookApp | |
Google+ | 103926722020369884651 |
Youtube | UCcr9tciZbuvJrEVAgIXCp8Q |
Kafin kace kwabo wannan shafi ya samu ƙarɓuwa wajen sauran ɗalibai kimanin 1200 na jami'ar ta Harvard. Kuma cikin wata guda rabin ɗaliban dake karatun ƙaramin digiri na jami'ar sunyi rajista da shafin na Facebook. Haka dai wannan shafi ya rinƙa samun karɓuwa daga ɗalibai daga wannan jami'a zuwa wancan.
A shekarar 2005 ne kuma aka yiwa shafin rajista a matsayin facebook.com akan kuɗi Dalar Amirka dubu ɗari biyu. A watan satumban shekara ta 2005 kuma shafin na facebook ya isa ƙasar Birtaniya kafin zuwa sauran ƙasashen duniya. Kuma kyauta ne dai ake rajistan shafin na facebook.
Amma kuma don gane da hanyoyin samun kuɗi kuwa. Shafin wanda ya zama kanfani na samun kuɗaɗen sa ne daga tallace tallace da manyan kanfanoni da ƙanana keyi domin sayar da hajar su ga masu anfani da shafin ta facebook. Yanzu dai kanfanin da aka fara da Dalar Amirka dubu ɗari biyu, kanfanonin sadarwa irin su Google da Yahoo sun taya shi akan kuɗi Dala biliyan 2, wanda kuma Mr. Zuckerberg yace albarka.
A shekarar 2004 an fara wata shari'a tsakanin Zuckerberg da kuma wasu masu mallakan kanfanin yanar sadarwa ta Connect U, wa'yanda ke zargin Zuckerberg da sace basirar kanfanin su, a lokacin da suka nemeshi daya shirya masu tsarukan shafin sadarwan su, a matsayin sa na kwararre a harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa a lokacin da dukkannin su ke ɗalibta a jami'ar ta Harvard koda yake tuni kotu tayi watsi da ƙarar a sabili da rashin cikakken sheda a shekarar 2007. Kuma kamar yadda wani shafin sadarwa shima na Wekepidia ta bayar yanzu haka dai akwai miliyoyin jama'a dake anfani da shafin ta Facebook da yawan su ya haura miliyan 350 a duniya.
<<>>> <<>>