Kagara

Ƙaramar hukuma ce a Nigeria

Kagara gari ne dake a ƙaramar hukumar Rafi a cikin jihar Neja, dake Najeriya, Kagara na cikin Gundumar Sanatan Neja ta gabas, kuma ita ce mazaunin Masarautar Kagara. Sauran manyan masarautun guda biyu a jihar sune Masarautar Minna da Masarautar Suleja,kowannensu na tsammanin wakilcin siyasa a jihar idan ba a matakin kasa ba. A farkon shekarata 2010 gwamnatin jihar ta kori shugaban ƙaramar hukumar Rafi.[1] sannan ta kafa kwamitin bincike don binciko ayyukan ƙaramar hukumar a lokacin da yake kan karagar mulki.A watan Disambar shekarar 2010, wata Babbar Kotun jahar Minna ta ba da umarnin a mayar da shi bakin aikinsa.

Kagara

Wuri
Map
 10°11′04″N 6°15′12″E / 10.1844°N 6.2533°E / 10.1844; 6.2533
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Neja
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Tattalin arziki gyara sashe

Garin yana da masana'antar sarrafa talc. An fara gina madatsar ruwa a shekarar 1979 a kan kudi naira biliyan 5. Jami'ar Fasaha ta Tarayyar Minna ce ta gudanar da aikin tantance tasirin muhalli na Hukumar Kula da Kogin Neja da Hukumar Raya Karkara (UNRBDA). An biya kusan N3 biliyan a watan Fabrairun shekarar 2002, lokacin da Ministan Albarkatun Ruwa, Muktar Shagari, ya ba dan kwangilar wa’adin kammala aikin dam din zuwa Disamba na shekarar. A watan Fabrairun shekarar 2004, Karamin Ministan Albarkatun Ruwa, Mista Bashir Ishola Awotorebo ya ziyarci wurin da aka gina madatsar ruwan, kuma sakamakon haka ya kira dan kwangilar da ya yi bayani kan jinkirin da aka samu a aikin. A watan Agustan shekarar 2004, yayin gabatar da famfunan hannu guda 500 daga Gwamnatin Tarayya zuwa ga Gwamnan Neja, Abdulkadir Kure, Mukhtar Shagari ya ce za a iya fuskantar aikin dam din saboda rashin amincewa da kason kasafin kudin. A watan Agustan shekarar 2007, Bala Kuta na All Nigeria Peoples Party, wakilin Majalisar Dokoki ta Kasa, ya yi alkawarin taimaka wa aikin madatsar ruwan.

Ta'addanci gyara sashe

An kashe dalibi daya kuma dalibai 27, malamai uku,'yan uwa goma sha biyu)' yan fashi suka sace a ranar 17 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

ƙabila gyara sashe

ƙabilar Hausawa


Masurata gyara sashe

Akwai masarauta a cikin garin Kagara masarautar babbar masarauta ce tunda Sarkin Kagara yana a matsayin Emir na duk wata masarauta dake a ƙaramar hukumar ko kuma yankin siyasar Neja ta gabas kenan.[2][3][4][5] a tarihin masarautar tanada sarakuna 3 na farko har zuwa yanzu don ƙarin bayani akan masarautar Masarautar Kagara

Dam ɗin Kagara gyara sashe

Garin yana da masana'antar sarrafa talc. An fara gina madatsar ruwa a shekarar 1979 akan kuɗi naira biliyan biyar. Jami'ar Fasaha ta Tarayya Minna ta gudanar da kimanta tasirin Muhalli ga Babban Kogin Neja da Hukumar Raya Karkara (UNRBDA). Kimanin Naira biliyan uku aka biya a watan Fabrairun shekara ta 2002, lokacin da Ministan Albarkatun Ruwa, Muktar Shagari, ya bai wa ɗan kwangilar wa'adin kammala madatsar ruwan zuwa watan Disamba na wannan shekarar. A watan Fabrairun shekara ta 2004 Ƙaramin Ministan Albarkatun Ruwa, Mista Bashr Ishola Awotorebo ya ziyarci wurin madatsar ruwan, a sakamakon haka ya kira ɗan kwangilar da ya yi bayanin jinkirin aikin. A watan Agustan 2004, yayin da yake gabatar da famfunan hannu guda 500 daga Gwamnatin Tarayya ga Gwamnan Jihar Neja, Abdul-ƙadir Kure, Mukhtar Shagari ya ce aikin dam ɗin zai iya lalacewa saboda rashin amincewa da kasafin kuɗin. A watan Agusta na 2007, Bala Kuta na Jam'iyyar ANPP wakilin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya yi alƙawarin taimakawa da aikin madatsar ruwan.[6]

Manazarta gyara sashe

  1. Nnadozie, Chinwendu (19 May 2010). "Nigeria: Court Reinstates Sacked Rafi LG Boss". allafrica.com. Retrieved 8 January 2022.
  2. Olufemi, Alfred (2 March 2021). "Emir of Kagara is dead". premiumtimesng.com. Retrieved 8 January 2022.
  3. Laleye, Dipo (21 June 2010). "2010: Can IBB's ambition upset calculations in Niger?". www. tribune.com.ng. Archived from the original on 14 March 2012. Retrieved 8 January 2022.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  4. Orintunsin, Jede (20 March 2010). "Battle of the emirates in Niger". The nation.net. Archived from the original on 9 May 2012. Retrieved 8 January 2022.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  5. Asishana, Justina (8 April 2021). "Kagara Emirate gets Emir". Retrieved 8 January 2022.
  6. William Fagg, Herbert List (1990). Nigerian images. National Commission for Museums & Monuments. p. 24. ISBN 0-85331-566-3.CS1 maint: uses authors parameter (link)