Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'Ikamatus Sunnah (JIBWIS). ƙungiyar addinin Musulunci ce, mabiya Sunnan Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi. Sannan kuma an kafa wannan ƙungiyar ne a babban Birnin Jihar Plato dake Jos wanda babban malamin Musulunci kuma Babban Hafsan Sojan Najeriya ya kafa, wato Sheikh Ismaila Idris Bin Zakariyya Jos[1] wanda kuma har yanzu Cibiyar Gudanarwa na ƙungiyar yana garin Jos a ƙarƙashin jagorancin Khalifa na farko na wannan ƙungiya wato Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir[2] wanda kuma har yanzu Cibiyar Gudanarwa na kungiyar yana garin Jos a karkashin jagorancin Khalifa na farko na wannan ƙungiya wato Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir[3]

Izala
Bayanai
Iri Tsarin Siyasa da Islamic organization (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Ideology (en) Fassara Salafiyya
Mulki
Hedkwata Jos
Tarihi
Ƙirƙira 1978

Ƙungiya ce da aka kafa ta da manufar yaƙi da bidi'o'i, wato ƙirqire-ƙirqire a cikin addini da kuma tabbatar da biyayya ga Annabi Muhammadu (Aminci Allah ya kara tabbata a gare shi) tare da abubuwan da ya zo da su daga Allah Maɗaukakin Sarki, ba tare da daɗi ko ragi ba.

Kamar yadda ƙungiyoyi masu kawo sauyi da gwagwarmaya a duniya suka sha wuya da suka daga hannun jama'a a karon fari, ita ma ƙungiyar Izala ta sha fama da irin wadannan matsaloli, amma daga baya ta yi nasara wajen kafa tsayayyen tsarin bin hanyar addinin Islama, ta yadda har wasu ƙungiyoyin da su ka fi ta daɗewa su ka dawo suna koyi da ita.

Muhimmam Manufofin Ƙungiyar gyara sashe

Daga cikin muhimman manufofin wannan ƙungiya sun hada da:

1. Kaɗaita Allah da bauta ba tare da haɗa Shi da wani ba (shirka). Sannan a tabbatar da biyayya ga Annabi Muhammadu (S.A.W) ba tare da jayayya ko kawo maganganun wasu mutane na daban ba.

2. Tabbatar da bin ɗabi'un (sunna) Manzon Allah (S.A.W) ba tare da ƙirƙire-ƙirƙire ba.

3. Watsi da dukkan al'adun da suka saɓa ma addinin Islama.

4. Soyayyar Annabi (S.A.W) da iyalan shi da sahaban shi /abokan shi da kuma surukan shi ba tare da sukar ko ɗaya daga cikinsu ba.

5. Tabbatar da neman ilimin addini da na boko a ko'ina a faɗin duniya tare da bin dokokin addini.

6. Tabbatar da mutuncin waliyyan Allah na gaskiya da salihan bayi da duk sauran mutanen kirki.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta gyara sashe

  1. https://gazettengr.com/gombe-governor-inuwa-yahaya-preaches-unity-seeks-prayers-for-nigerian-leaders/
  2. https://dailypost.ng/2022/05/01/2023-vote-for-competency-not-religion-or-political-parties-cleric-tells-'''Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'Ikamatus Sunnah''' ('''JIBWIS'''). ƙungiyar addinin [[Musulunci]] ce, mabiya [[Sunnah|Sunnan]] Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi. Sannan kuma an kafa wannan ƙungiyar ne a babban Birnin Jihar [[Plateau (jiha)|Plato]] dake [[Jos]] wanda babban malamin Musulunci kuma Babban Hafsan Sojan [[Najeriya]] ya kafa, wato Sheikh [[Ismaila Idris Bin Zakariyya]] Jos<ref><nowiki>https://gazettengr.com/gombe-governor-inuwa-yahaya-preaches-unity-seeks-prayers-for-nigerian-leaders/
  3. https://dailypost.ng/2022/05/01/2023-vote-for-competency-not-religion-or-political-parties-cleric-tells-nigerians/