Rashidi Yekini

Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya

Rashidi Yekini An haifi marigayi Rashidi Yekini ne a garin Kaduna dake arewacin Najeriya, a ranar 23 ga watan Oktoba shekararekarar ta 1963.

Rashidi Yekini
Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna, 23 Oktoba 1963
ƙasa Najeriya
Mutuwa Jahar Ibadan, 4 Mayu 2012
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
CA Bizertine (en) Fassara-
Shooting Stars SC (en) Fassara1982-19845345
Abiola Babes (en) Fassara1984-1987
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya1984-19985837
Afrika Sports d'Abidjan1987-1990
Vitória F.C. (en) Fassara1990-199411490
Olympiacos F.C. (en) Fassara1994-199542
  Sporting Gijón (en) Fassara1995-1996143
Vitória F.C. (en) Fassara1997-1997143
  FC Zürich (en) Fassara1997-19982814
CA Bizertine (en) Fassara1998-19992814
Al-Shabab Football Club (en) Fassara1999-19992814
Afrika Sports d'Abidjan1999-20022814
Bridge F.C. (en) Fassara2002-20032814
Gateway United F.C.2005-2005267
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Nauyi 80 kg
Tsayi 190 cm
Imani
Addini Musulunci

Fara tashen sa

gyara sashe
 
ya fara tashe

Yakini tun yana da shekarun haihuwa 18 ya soma taka leda a babban mataki inda ya fara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta UNTL dake garin Kaduna a shekarar ta 1981.

Bayan shekaru kusan biyu sai ya koma ƙungiyar Shooting Stars ta garin Badin wato jihar Oyo, daga nan kuma ya koma Abiola Babes daga shekarar 1984 zuwa 1987.

Rashidi Yekini ya tafi ƙasar Ivory Coast inda ƙungiyar Africa Sports ta siye shi don ya murza mata leda, kuma ya shafe shekaru uku a ƙasar kafin ya tsallaka Turai a shekarar 1990 lokacin da ƙungiyar Victória Setúbal ta ƙasar Potugal ta siyeshi.

Kuma a kakar wasa ta shekarar 1993 zuwa 1994, Yekini ya kasance ɗan ƙwallon da yafi kowa cin kwallaye a gasar ƙwallon Portugal, inda ya zira kwallaye 34 cikin wasanni 32.

A shekarar 1994 kuwa, Rashidi Yekini ya koma ƙasar Girka ne da taka leda inda ƙungiyar Olympiacos ta siyeshi.

Daga nan kuma ya koma murza leda a gasar La Liga tare da Sporting Gijon amma bayan shekara guda sai ya kara komawa tsohuwar ƙungiyar ta Portugal wato Vitoria Setubal.

A shekarar 1997, Yekini ya koma FC Zurich ne a Switzerland.

A shekarar 1998 kuwa sai ya koma ƙwallonsa a ƙasar Tunisiya tare da Athlétique Bizertin, daga nan kuma sai ya koma ƙungiyar Al-Shabab dake Riyad a ƙasar Saudiyya.

A shekerar 1999 kuwa, angulu ce ta koma gidanta na tsamiya, saboda Rashidi Yekini ya kara komawa ƙungiyar ta Afrca Sports ne a Ivory Coast, kuma bayan karin wasu shekaru uku, sai ya dawo Najeriya inda ya bugawa kungiyoyin Julius Berger da kuma Gateway FC ta Abeokuta inda anan yayi ritaya a shekara ta 2005.

Nasarorin sa

gyara sashe

A bangaren Super Eagles kuwa, Rashidi Yekini ya zira kwallaye 37 a wasanni 58 da ya bugawa Najeriya, wanda kuma a tarihi har izuwa yanzu babu wani ɗan ƙwallon Najeriya da ya zira kwallaye masu yawan nasa.

Ya kuma halarci gasar cin kofin ƙwallon duniya sau biyu wato a Amurika a shekarar 1994 da kuma Faransa a shekarar 1998.

Har ila yau Rashidi Yekini ne ya ciwa Najeriya ƙwallonta na farko a gasar cin kofin duniya, wato ƙwallon daya zira a ragar Bulgaria, wanda a karshe Najeriya ta samu nasara daci uku.

Rashidi Yekini kuma ya halarci gasar cin kofin ƙwallon Afrika da dama hadda na shekarar 1994 a ƙasar Tunisia inda ya taimakawa Najeriya ta lashe gasar.

Abinda kuma yasa aka bashi gwarzon ɗan ƙwallon Afrika a wannan shekarar saboda irin namijin kokarin da yayi da kuma sadaukar da kai.

Sannan kuma ya bugawa Najeriya ƙwallo a gasar Olympics da aka yi a birnin Seoul a shekarar 1988.

Rasuwar sa

gyara sashe

Rashidi Yekini ya rasu a ranar Juma'a hudu ga wannan watan a garin Ibadan na jiyar Oyo dake kudancin Najeriya yana da shekaru 48 , kuma kafin rasuwarsa yayi fama da rashin lafiya.


Kungiyoyin da ya bugama wasa Rashidi Yekini ya buga wasan ƙwallon ƙafa :