Kaduna (birni)
Kaduna birni ne, da ke jihar Kaduna, a ƙasar Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Kaduna. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006, jimillar mutane dubu dari bakwai da sittin, amma bisa ga kimantawa a shekarar 2017, jimilar mutane miliyan ɗaya da dubu dari huɗu. Birnin Kaduna kilomita dari biyu ne daga Abuja. Sannan kilomita saba'in da wani abu daga zaria. Kaduna na akan kogin Kaduna ne. Muhimman wuraren da ke cikin garin Kaduna sun hada da gidan tarihi na sardaunan sokoto wato sir Ahmadu Bello, Masallacin Sarkin Musulmai Bello, gidan tarihi na kasa, gidan gwamnatin jihar Kaduna, makarantar horar da Sojojin na Najeriya manyan da kanana, dadai sauran su.
Kaduna | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Suna saboda | Kogin jihar Kaduna | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Kaduna | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 760,084 (2006) | |||
• Yawan mutane | 1,763.54 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 431,000,000 m² | |||
Altitude (en) | 250 m | |||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 1913 | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | kadunastate.gov.ng |
Hotuna.
gyara sasheWasu hotuna kenan na sassa a cikin birnin Kaduna
-
Daya cikin manyan Masallatan dake cikin garin Kaduna
-
Hasumiyar masallacin Sultan Bello
-
Masallacin da yamma
-
Cikin garin Kaduna da daddare
-
Motar haya a tashar NDA Badarawa .
-
Babban hanyar data ratsa cikin garin Kaduna mai suna Ahmadu Bello Way.
-
Motar kwashe shara dan tsaftace cikin garin Kaduna
Ilimi.
gyara sasheGarin Kaduna gari ne mai dimbin tarihi na masana littattafai musamman ilimin addini da na boko. Akwai makarantu daban daban a birnin kaduna.