Girka ( Arabic and Ajami[1] غرك), ɗan ƙauye ne a ƙasar Kaita[2] da ke Jihar Katsina.[3] Tarihi ya baiyana cewa asalin kafuwar wannan ƙauye ya biyo bayan gudun hijira da wasu iyalai suka yi daga ƙasar Sakkwato[4] can tun kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka a ƙasar Hausa.

Wikidata.svgGirka

Tarihin kunne ya girmi kaka ya nuna cewa, wannan iyali suna zaune ne tare da manya a Sakkwato har zuwa lokacin da Sarkin Musulmi na wancan lokaci ya nemi ya basu sarauta. Amma saboda kamewa da ƙanƙan da kai sai waɗannan iyalai suka janye jikinsu cikin ruwan sanyi daga karɓar wannan sarauta. Bayan ganin yanda Sarki ya nace kan yi masu sarauta, sai suka yanke shawarar sulalewa su bar masa ƙasarsa. Daga nan ne suka yo yamma da "sauri."Kwanci tashi ne suka isa cikin ƙasar Kaita kuma suka nosa har zuwa kusa da wani rafi da ake kira Taukin Girka.A nan ne waɗannan iyali suka ci gaba da zama har zuwa yau. Sunan mai sarautarsu Magaji Sauri, kuma wannan ya samo asali daga 'sauri' ko hanzarin da suka rinƙa yi a lokacin da suka baro ƙasar Sakkwato.

"'Girka"'kuma tana nufin 'ajiye wani abu a wani muhalli' kenan dai Allah ne ya girkasu a wannan ɗan wuri mai albarkar ƙasa ta wajen kiwo,noma da aikin lambu. A yanzu wannan ƙauye ya zama gari domin kuwa Magaji Sauri shi ne Wakilin Sarkin Sulluɓawa. Sarkin Sullubawa shi ne mai sarautar duk Ƙasar Kaita baki ɗayanta kuma shi ɗan Sarkin Katsina Muhammadu Kabir ne. Ko bayan haka,akwai ƙauyuka da dama dake ƙarƙashin Girka. Misali, Maƙaurachi, Tarkama, Garu, Kwangwami da sauransu. Akwai wuraren tarihi a ƙasar Girka. Akwai wata atsabibiyar bishiya wadda ba'a zuwa wurinta da rana tsaka saboda ƙwanƙwamanta. Har yanzu Taukin Sauri na nan kuma duk shekara ana zuwa kamun kifi kamar yanda ake yi tun zamanin baya.

Cigaban zamani ya ratsa ƙasar Girka domin yanzu suna da makarantun piramare a Hedikwata Girka da kuma yawancin ƙauyukan dake ƙarƙashin ƙasar.An gina asibiti da ɗakunan malaman asibiti. Shekarun baya kuma an gina makarantar gaba da piramare wanda yanzu har sun soma yaye 'yan aji uku. Girka ta samar da mutanen da ake alfahari dasu a ƙasar Kaita ta ɓangarori daban-daban wanda ya haɗa da ilimin boko, kasuwanci da kuma siyasa.

Babbar sana'ar mutanen wannan ƙasa ba ta wuce noma da aikin lambu. Suna kiwo daidai gwargwado kuma matasansu na fita zuwa manyan biranen Nijeriya domin aikin ƙwadago ko kasuwanci. Sukan je Ikko (Lagos), Abuja, Patakwal (Port-Harcourt), Naija (Niger) da Kaduna.

Akalla ansamu shuwagabanin wannan kauye guda goma sha ukku akan wannan yagada yarasu wani yagada kuma dukansu familin fulanin zaure ne kuma har yanzu haka suke rike da masarautar ta Girka kuma itace babbar masarauta mai cikakken milki mai sanda ta daya a kasar Kaita.

haka take kuma mutanan garin Girka tin asali masu rikone ga adinin Muslinci kuma masu biyayane ga shuwagabannin su

ManazartaGyara

  1. Ajami, Rubutun Hausa amman da baƙaƙen Larabci. http://www.saudiaramcoworld.com/issue/201105/from.africa.in.ajami.htm
  2. Ƙaramar Hukumar Kaita. http://en.m.wikipedia.org/wiki/Kaita,_Nigeria
  3. Jahar Katsina, Nijeriya. http://en.m.wikipedia.org/wiki/Katsina_State
  4. Daular Usmaniyya ta Sakkwato. en.wikipedia.org/wiki/Sokoto_Caliphate