Kannywood ko kuma Hausa Sinima, Itace masana'antar fina-finai na Harshen Hausa da ke a arewacin Najeriya. Cibiyarta na nan a cikin birnin Kano da kuma sauran wasu jahohin Najeriya kamar irin su Jos, Kaduna, Katsina da sauransu.

Kannywood
film genre (en) Fassara da cinema by country or region (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Nollywood
Suna saboda Kano da sinimar Amurka
Nahiya Afirka
Language used (en) Fassara Hausa
Ali Nuhu Babban Jarumi kuma sarki a kannywood
Hadiza Aliyu Gabon Babbar Jaruma Ce A Kannywood
Momee Gombe Jarumar Kannywood
Hajiya Hadiza Muhammad 'Hadizan Saima'
Jarumi Adam A Zango
Jarumi Kuma Mawaƙi Yakubu Muhammad

Kannywood

gyara sashe

Kannywood sunan arone dake nufin sinima a harshen Hausa. Wani ɓangare nena babbar siniman Najeriya mai suna Nollywood, wanda ya ƙunshi sauran cibiyoyin shirya fina-finai na harsunan Najeriya da dama. Sunan "Kannywood" kalma ce da aka ƙirƙira daga kalmomi biyu; Kano da Hollywood - kamar dai cibiyar Fina-finan Ƙasar Amurka Hollywood."Kannywood" ta samo asali ne daga ƙarshen shekarar, alif Ɗari tara da casa'in da tara 1990, lokacin da Sanusi Shehu na Mujallar Tauraruwa ya ƙirƙiri kalmar Kannywood sannan kalma tayi fice a matsayi sunan da ake kiran masana'antar a Arewacin Najeriya. An ƙirƙiri kalmar "Kannywood" a shekara ta, 1999, shekaru uku kafin ƙirƙiran kalmar Nollywood.[1]

Marubuta Waƙoƙi da mawaƙa waɗanda ke shirya ko yin waƙa a finafinan Hausa sun haɗa da Nazifi Asnanic,[2][3] Naziru M Ahmad,[4] Ali Jita,[5][6] da Fati Nijar.[7][8] Umar M Shareef.[9].

Suka da malaman Musulunci

gyara sashe

A shekara ta, 2003, tare da sanuwar kungiyar Izala da kuma hawa karagar mulki na Ibrahim Shekarau, gwamnatin masu tsananin kishin addini na Kano ta fara wani kamfe na nuna adawa ga masana'antar ta Kannywood. Yawancin fina-finai da ake ganin ba sa bin tsarin na addini, an tantance su kuma an daure wasu masu shirya su. Wannan ya jawo cikas ga nasarorin da Kannywood ta samu kuma ya ba masana'antar fim ta Kudancin Najeriya damar samun nasarori fiye da ita.

Matsaloli da gwamnati.

gyara sashe

A cikin shekara ta, 2007, tsiraicin Hiyana : lokacin da faifan batsa na wata fitacciyar 'yar fim ya fito fili ya haifar da mummunan martani daga gwamnatin Islama ta wancan lokacin ta Jihar Kano a ƙarƙashin gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau. Ibrahim Shekarau ya naɗa Babban Darakta a hukumar tace fina-finai, Abubakar Rabo Abdulkareem tare da goyon bayan ƙungiyar Izala da sauran ƙungiyoyin masu kishin Islama, an tantance Fina-finan Kannywood da wasu shahararrun masana'antun littattafan soyayya na harshen Hausa, an kuma daure jaruman fim, marubuta da dai sauransu, sannan Gwamna da kansa ya ƙone Sauran kayan aikin shirye-shirye.[10] A shekara ta, 2011, maye gurbin gwamnatin Islama da mafi sassaucin gwamnati ƙarƙashin jagorancin PDP ya haifar da kyakkyawan yanayi ga masana'antar. A shekara ta,2019, biyo bayan sake zaɓen gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano, hukumar kula da takunkumi ƙarƙashin Sakataren zartarwa, Isma'il Na'abba Afakallahu ta ƙaddamar da wani sabon kamun na maƙada da 'yan fim. An kama wani daraktan fim din, Sanusi Oscar, da wani mawaƙi, Naziru M. Ahmad tare da kai su kotu kan zargin da ake musu na cewa sun saki waƙoƙi ba tare da izinin mai bincike ba. An bayar da belin mutanen biyu(2).[11] Ƙungiyar adawar ta Kwankwasiyya ta bayyana cewa kamun na da nasaba da siyasa saboda ana ɗaukar waɗanda ake zargin a matsayin masu nuna goyon bayan Jam’iyyar ta PDP a zaɓen da ya gabata.[12].

Manazarta.

gyara sashe
  1. {{Cite web|url=http://nigerianstalk.org/2012/10/09/kannywood-the-growth-of-a-nigerian-language-industry-carmen-mccain-2/%7Ctitle=Kannywood[permanent dead link], the growth of a Nigerian language industry–Carmen McCain|last=McCain|first=Carmen|date=9 October 2012|access-date=1 May 2021|ar

    Fina-finan Hausa

    gyara sashe

    Fim din hausa da sannu a hankali ya samo asali ne daga shirye-shiryen RTV Kaduna da gidan Radiyon Kaduna a cikin shekarun 1960. Kwararru kaman Dalhatu Bawa da Kasimu Yero suka fara gabatar da wasannin kwaikwayo wanda ya zama sananne ga masu sauraro a Arewa. A shekarun 70 zuwa 80,

    , Usman Baba Pategi da Mamman Ladan suka fara gabatar da Wasannin Barkwanci na Hausa ga masu sauraro a Arewacin Najeriya.

    1990s:Tasirin Bollywood

    gyara sashe

    A sama muhimmin canji a finafinan harshen hausa a shekarun 1990 tare da zimman jawo hankalin masu kallan shirya-shiryan hausa wanda suke da ra'ayin fina-finan Bollywood, Fina-finan Kannywood; Ya zamanto kamanceceniya tsakanin al'adun sinima na kasar Indiya da na Hausawa kuma ya shahara ya kuma samu karmuwa matuka.Turmin Danya ("The Draw"), 1990, shine shirin fim na Hausa da ake dauka a matsayi fim na farko da aka fara cin nasara a tarihi Fina-finan Kannywood. Wasu fina-finai kamar Gimbiya Fatima, In Da So Da Kauna, Munkar, Badakala da Kiyarda Da Ni sun biyo bayan shi. Sabbin ‘yan wasa kamar su Ibrahim Mandawari da Hauwa Ali Dodo sun shahara kuma sun kafa fagen fitowar tauraruwa kamar 'yan mata daga baya.

    2000s Kannywood

    gyara sashe

    Zuwa shekara ta 2012, sama da kamfanonin finafinai 2000 suka yi rijista da kungiyar Masu shirya Fina-finai na Jihar Kano.

    Wani kwamitin tantancewa na gidauniyar masu shirya Fina-finan Kanywood da kuma 'yan kasuwa sun kirkiri wata kwamiti a karkashin mulkin Gwamna Rabiu musa Kwankwaso, a matsayin Hukumar Tace Fina-finai a shekara ta 2001. An nada Mista Dahiru Beli a matsayin Sakataren zartarwa na farko na gungiyar.<ref>Samfuri:Cite . news

  2. "Nazifi Asnanic [HausaFilms.TV - Kannywood,Fina-finai,Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Retrieved 2020-02-14.
  3. "Kannywood's finest, worst moments of 2014 - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2015-01-01. Retrieved 2020-02-14.
  4. "Kannywood singer, Naziru Ahmed, weds - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2014-01-07. Retrieved 2020-02-14.
  5. "Ali Jita [HausaFilms.TV-Kannywood,Fina-finai,Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Retrieved 2020-02-14.
  6. Liman, Bashir; Abuja (2018-10-27). "Ali Jita holds concert, launches war against cancer". Daily Trust (in Turanci). Archived from the original on 2019-02-15. Retrieved 2020-02-14.
  7. "Lafiyata kalau —Fati Nijar". BBC News Hausa. Retrieved 2020-02-15.
  8. "Singer Fati Nijar turbanned 'queen of Hausa singers in Europe'" (in Turanci). 2019-11-25. Retrieved 2020-02-15.
  9. Nura m InuwaShareef, Umar. "Why I dumped music for acting — Abdul Shareef". Retrieved 2017-11-04.
  10. Samfuri:Cite. web
  11. "Kano singer, Sarkin Wakan arrested over alleged anti-Ganduje songs". Retrieved February 18, 2020.
  12. Muhammed, Isiyaku (September 12, 2019). "Kwankwasiyya reacts,as Police arrest popular Kano singer,Sarkin Wakar". Daily Trust. Archived from the original on December 26, 2019. Retrieved February 18, 2020.