Sani Musa Danja

Dan wasan kwaikwayo na hausa sannan kuma mawaki

[1]

Sani Musa Danja
Rayuwa
Cikakken suna Sani Musa Abdullahi
Haihuwa Fagge, 20 ga Afirilu, 1973 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a Jarumi
Imani
Addini Musulunci

Sani Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Sani Danja ko kuma Danja {An haife shi a ranar 20 ga watan Afrilu shekaralif ɗari tara da saba'in da Uku1973} Miladiyya. jarumin fim ne a Nijeriya, furodusa, darekta, mawaƙi kuma mai rawa.[2][3] Yana fitowa a finanin masana'antar Kannywood da kuma na kudancin Najeriya Nollywood..[4] A watan Afrilun shekara ta dubu biyu da Sha takwas 2018 Etsu Nupe, Yahaya Abubaka ya nada shi a matsayin Zakin Arewa.[5][6] Ya kasance ɗaya daga cikin shahararrun yan wasan kwaikwayo a Kannywood

Aiki gyara sashe

Ya shiga harkar finafinan Hausa a shekarar 1999 a amatsayin dalibi. Danja ya fito a fina-finai da dama irin su, Manakisa, warya tabi Kwarya, Jaheed, Nagari, Wasiyya, Harsashi, Gidauniya, Daham, Jarida, Matashiya, da sauransu. A shekarar 2012 ya fara haskawa a Nollywood'Yar Kogin.[7][8]

Fina-finai gyara sashe

Sani Musa Danja ya yi, ya shirya kuma ya ba da umarni a fina-finan Kannywood da Nollywood . Daga cikinsu akwai: [9]

Sunan Fim Shekara
Yar agadez 2011
A Cuci Maza 2013
Albashi (Albashi) 2002
Bani Adam 2012
Budurwa 2010
Da Kai zan Gana 2013
Daga Allah ne '' (Daga Allah ne) 2015
Daham 2005
Dan Magori 2014
Duniyar nan 2014
Fitattu 2013
Gani Gaka 2012
Gwanaye 2003
Hanyar Kano 2014
Kukan Zaki (Kukan zaki) 2010
Daya bangaren 2016
Buri uku a duniya (Buri guda uku a duniya) 2016

Iyali gyara sashe

Sani danja ya auri Mansura Isah Allah ya azurta su da ƴaƴa huɗu.

Manazarta gyara sashe

  1. "Kannywood actor, Sani Danja Turbaned as Zaki Af Arewa". Modern Ghana. 26 April 2018. Retrieved 21 January 2019.
  2. Blueprint (2017-10-14). "It pains how people download our films – Danja". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2020-09-24.
  3. "Culture bane of Kannywood - Sanni Danji, Hausa actor". Vanguard News (in Turanci). 2010-10-15. Retrieved 2022-07-17.
  4. "Nollywood – Kannywood Scene". Retrieved 5 February 2019.
  5. "Kannywood actor, Sani Danja Turbaned as Zaki Af Arewa". Modern Ghana. 26 April 2018. Retrieved 21 January 2019.
  6. "Kannywood: Sani Danja turbaned by Etsu Nupe". Premium Times Nigeria. 10 August 2017. Retrieved 21 January 2019.
  7. "Kannywood Star Actor Becomes Richest Northern Entertainer". Pulse Nigeria (in Turanci). 2014-09-26. Retrieved 2020-09-24.
  8. "Kannywood actor, Sani Danja, makes Nollywood debut". Premium Times Nigeria. 1 September 2012. Retrieved 22 January 2019.
  9. "Sani Danja [HausaFilms.TV – Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Retrieved 23 January 2019.