Umar M Shareef

Mawaƙin hausa a najeriya

Umar Muhammad Shareef An fi saninsa da Umar M Shareef (An haife shi a shekara ta alif 1989) a cikin garin Kaduna. Fitaccen mawakin Hausa ne na soyayya haka nan kuma mai shirya fina finan Hausa kuma jarumi a masana'antar ta Kannywood.

Umar M Shareef
Rayuwa
Haihuwa 1989 (34/35 shekaru)
Sana'a
Sana'a mawaƙi da Jarumi
JS_Icon_Edit
JS_Icon_Edit

Umar M Shareef, fitaccen mawakin Hausa ne, na soyayya, sannan an san shi a matsayin jarumi a masana'antar Kanywood. Umar M Shareef yana da kyakkyawar alaka da dukkan yan wasan kwaikwayon Hausa na Kanywood musamman Ali Nuhu wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen fito da jarumin, sannan ya samu lambar yabo daga bangare daban-daban.

Tarihi gyara sashe

An haifi jarumin a shekarar 1989 a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, shahararren mawakin Hausa ne sannan kuma jarumi ne a masana'antar kannywood wanda ya shahara a kasar Najeriya da sauran kasashen afrika. Jarumi kuma mawaki yana da mabiya a kasashe da dama a fadin duniya, Wanda a kullum burinsa bai wuce ya ga ya burgesu ba.[1]

Karatu gyara sashe

Jarumin ya fara karatun Qur'ani tun yana yaro a gida kafin ya shiga makarantar boko wacce izuwa yanzu ya kai matakin digiri wanda ya ke yi a Jami'ar Jihar Kaduna (KASU)

Wakoki gyara sashe

Asalin fara wakarsa ta dalilin wata yarinya da yake so amma ya kasa sanar mata har izuwa lokacin da ya yanke shawarar tinkararta amma sai bata fito ba hakan ya sa ya tafi yana rera waka. Jarumin ya jima yana waka amma taurarinsa ya fara haskawa ne a shekara ta 2007 sannan yayi wakoki da dama a bangare daban-daban na soyayya, siyasa, da wakokin biki da suka haɗa da;

 • Jinin jikina
 • Sareena
 • Jirginso
 • Ruwan dare
 • Hafiz
 • Ciwon idanuna
 • Arewa
 • Ciwon so
 • Mariya
 • Wazana ba kaina

Albums/Kundi gyara sashe

Sannan yanzu yayi albums da dama kamar su:

Sunan Kundi/Album Shekarar fita
Bako 2018
Tsintuwa 2016
Masoya 2016
Kalaman bakina 2017
Ni Da Ke 2018
Babbar Yarinya 2017
Kuyi Hakuri 2017

Haɗaka gyara sashe

Sannan yayi wakoki da mawaka da dama kamarsu;

 1. Nura M Inuwa
 2. Lilin Baba
 3. Abdul D one
 4. Hamisu Breaker
 5. Adam A Zango da sauransu.

Fina-finai gyara sashe

Ya fito a finafinai da dama kamarsu;

 • Mansoor
 • Sareena
 • Mujadala
 • Hafeez
 • Mariya
 • Tsakaninmu
 • Ciwon idanu na
 • Kar ki manta Da ni
 • Nass

Bugu da kari mafi yawan fina-finansa ya fito ne a companin FKD wanda mallakin Ali Nuhu ne. Sannan shi ne mamallakin Shareef studio wanda sun shirya fina-finai kamar su

 • Zarah
 • Jinin jikina

Karramawa gyara sashe

Jarumin ya sha karban kyautar karramawa da kyautar girmamawa da dama a fadin duniya daga kungiyoyi da dama kamar su

 1. Kannywood films award
 2. Afrikan actors

Da sauransu

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Ya kasance daga cikin manyan jaruman da suka ziyarci sassa daban-daban na duniya. Jarumin ya ziyarci kasashe da dama wadda suka haɗa da : Niger, Ghana, Cameron, Chad, da sauransu.[ana buƙatar hujja]

Iyali gyara sashe

Umar M Shareef yana da mata daya Maryam da yara biyu jarumin da kuma Hafsat.

Manazarta gyara sashe