Ali Jita
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Ali Isah Jibrin (Haihuwa: A ranar 5, ga watan Yulin shekara ta alif 1983) Ana masa laƙabi da Ali Jita a fannin waƙa, ana kuma kiran shi da Mai jita ko Ali Isah Jita sunan shi na yanka shine 'Ali Isah Jibrin. Ya kasance mawakin Hausa na zamani, marubucin waƙa kuma mai rerawa.[1][2][3] An haife shi a cikin jihar Kano a wani gari mai suna Gyadi gyadi, Ali jita ya tashi a Shagari quarters a karamar hukumar Kumbotso. Daga bisani kuma aiki ya mai da mahafinsu da su garin Lagos daga baya suka kara komawa Abuja. Sunan mahaifinsa Alhaji Sallau Jibrin Kibiya ya kasance mahauci ne, Mahaifiyarsa kuma Hajiya Ummul-Khairi.[4].
Ali Jita | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Ali Isah Jibrin |
Haihuwa | jahar Kano, 15 ga Yuli, 1983 (41 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Hausawa |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi, mai rubuta waka, darakta, producer (en) da mawaƙi |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Karatu.
gyara sasheAli jita ya fara karatun noziri a shagari quaters, yayi karatun firamari da sakandari a Victoria ireland dake Lagos a cikin wani barikin sojoji mai suna Bonikam Barrack, ya karasa karatun sa na sakandiri ne a Abuja. Sannan ya zurfafa karatunsa a Federal College of Education Kano inda ya karanta Public Administraion, inda aka bashi darajan shaidawa ta National Diploma, sannan kuma ya karanta ilimin kwamputa a Intersystem ICT School inda ya ƙara samun shaida na Diploma.[5]
Waka da fim.
gyara sasheYawancin wakokin Ali jita an saka su a masana'antar fim ta Kannywood, amman wasu daga cikin Albom ɗin shi kuma an sayar dasu ne a wajen Kannywood, Yana waka ne tare da shahararren mawaki Nazifi Asnanic da kuma Fati Nijar a matsayin abokan arziki. Harwa yau, shahararren mawakin yayi waka tare da Nazir M Ahmad mai suna Mama, sannan yayi waka tare da Umar M Shareef mai suna Kano. A shekara ta 2018, Ali jita yayi wata waka mai suna Love, wakar ta lashe lambar girma na jadawalin wakokin da suka fi kowanne a shekaran, a inda wakan tazo na biyu, kamar yanda BBC Hausa suka dauko rahoto.[6][7] Ali jita yayi amfani da salan Ingausa wajen rubuta wakan da kuma rerawa. A shekara ta 2019, yayi bidiyon wakan sa mai suna Arewa angel tare da tsohuwar jaruman Kannywood mai suna Rahama Sadau. Sannan yayi bidiyon waka mai suna Love tare da Hadiza Gabon.[8]
Rayuwa.
gyara sasheAli jita ya fara harkan waka tin yana ɗan shekara 16, a lokacin yana makarantan islamiyya a Lagos[4] tin lokacin da yake zurfafa karatun sa a Federal college of education kano ya kasance yana ɗan taɓa waka kadan-kadan. haka ya cigaba da taɓa waka har girman sa. ya kasance mutum ne mai saukin kai, yana da sanyayyar murya. Mutum ne kuma mai yawan murmushi. Yana san Nazifi Asnanic a matsayin abokin kirki a wajen waka da kuma cikinta. Kuma su biyun makusantan juna ne a harkan waka, sunyi wakoki dayawa tare irinsu Aboki da Ruwan zuma. An kira shi da Ali jita ne saboda san jita da yakeyi, kuma yana yawan rike Jita a wakokinsa da kuma ambatan sunanta. Ali jita yana da aure harda yara biyar, Usman suna kiranshi da Affan, da Aliyu inkiya Ramadan, Ahmad farid, zainab hidda sai Aisha ana kiranta da Afra.
Kundin Wakoki.
gyara sasheAlbom | Wakoki | Shekara | Adadin wakoki |
---|---|---|---|
Labarin duniya | * wacece nake so
|
12 | |
Zakin maza | *Rabbana
*Duniya *watan Azumi *Farar diya
|
2016 | |
Mata | *Mata | 2018 | |
Arewa Angel
Mamana Tarkon kauna Gimbiyar mata Buri uku Yar lele Duniya Halimatu sadiya Asha ruwa Jawabi Yara yara Kece Love Indo Aure Zaman aure Farar diya Zakka Mai jita Fati fati Kano |
Ba'a san shekaran ba |
Kambu da Lambar girma.
gyara sasheAli jita ya samu lamban girmamawa a fannin waka daban daban akalla guda goma sha biyar 15 kamar haka:
Sunan awad | Lamban girma | shekara |
---|---|---|
Ama award | ||
Tozali award | ||
MTN award |
Diddigin bayanai na waje.
gyara sashe- Ali jita da Nazifi Asnanic a wakan Aboki Ali jita ft Nazifi[permanent dead link]
- Ali jita da Nazifi Asnanic Ruwan Zuma jita ft Nazifi Asnanic Ruwan Zuma[permanent dead link]
- Ali jita ft Nazifi Asnanic da Naziru M Ahmad jita ft Nazifi Asnanic da Nazir M Ahmad[permanent dead link]
- Ali jita ft Rahama Sadau Arewa Angel jita ft Rahama Sadau Arewa Angel[permanent dead link].
- Wasu Daga Cikin Wakokin Ali Jita Archived 2022-02-12 at the Wayback Machine
Manazarta.
gyara sashe- ↑ https://www.bbc.com/hausa/news/2016/07/160711_kannywood_kalankuwa_sallah
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-02-15. Retrieved 2020-01-08.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-05-28. Retrieved 2020-01-08.
- ↑ 4.0 4.1 https://allafrica.com/stories/200809220641.html
- ↑ http://hausafilms.tv/musician/ali_jita
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/amp/labarai-46693772
- ↑ https://www.bbc.co.uk/hausa/labarai-46701664
- ↑ https://afrobitz.com/ali-jita-feat-hadiza-gabon-love-new-2018/amp/[permanent dead link]
- ↑ https://www.dailytrust.com.ng/author/belloabdulazeez/page/2117[permanent dead link]