Ibrahim Shekarau

Ɗan siyasar Najeriya

Malam Ibrahim Shekarau[1] tsohon Malami ne kuma ɗan siyasan Najeriya.[2] An haife shi a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da biyar (1955) Miladiyya, a garin Kano, Arewacin Najeriya (a jahar Kano). Ya riƙe Ministan ilimin Najeriya daga shekara ta 2014 zuwa shekarar 2015.[3] Ya fara takarar Gwamnan jahar Kano a shekara ta 2003, wanda daga bisani ya zamto ya lashe zaɓen da aka yi a watan Janairun shekarar 2003. Ya yi mulkin jahar har sau biyu sanadiyyar sake samun nasarar da yayi a zaɓen shekarar 2011, wanda haka ne ya kuma sa ya jagoranci mulkin jahar na tsawon shekaru 8. kafin nan Rabi'u Kwankwaso wanda yayi gwamna kafinsa ya sake dawowa shi ma a karo na biyu inda ya yi takarar matsayin gwamnan jahar a karo na biyu. Kwankwason yayi nasarar lashe zaɓen shi ma inda ya yi mulkin jahar a karo na biyu daga watan Mayun shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.

Ibrahim Shekarau
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023
Rabiu Kwankwaso
District: Kano Central
gwamnan jihar Kano

Mayu 2003 - Mayu 2011
Rabiu Kwankwaso - Rabiu Kwankwaso
District: Kano Central
Ministan Tsaron Najeriya

Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 5 Nuwamba, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Kanuri
Ƴan uwa
Abokiyar zama Amina ibrahim shekarau
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Hausa
Kanuri
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, anti-vaccine activist (en) Fassara da administrator (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa New Nigeria Peoples Party (en) Fassara
Malam Ibrahim Shekarau da wani bature

Zargin cin kudin makamai

gyara sashe
 
Ibrahim Shekarau

A halin yanzu Ibrahim Shekarau ya na fuskantar shari'a a gaban kotu bisa zargin haɗa baki da karkatar da kuɗi kimanin miliyan ɗari tara da hamsin (950,000,000) wanda wani ɓangare ne daga kudaden da gwamnati ta ware a shekarar 2014 don yaki da masu tada ƙayar baya amma aka karkatar da su a wancan lokacin don yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ofishin mai bada shawara akan harkokin tsaro na manzan lokacin, wato Sambo Dasuki ya fitar. Amma sai dai har yanzu ba'a kama shi da laifin ba.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.google.com/amp/s/www.bbc.com/hausa/articles/cp933ynr7zmo.amp
  2. https://www.bbc.com/hausa/news/2011/01/110119_shekarau_profile
  3. https://dailypost.ng/2024/02/16/insecurity-implement-2014-confab-report-shekarau-tells-tinubu/