Alhassan Saeed Adam Jos
Sheikh Dr. Alhassan Sa'eed Adam Jos (1956-2017) fitaccen malamin addinin musulunci ne a Najeriya, malami, kuma marubuci wanda ya shahara wajen bayar da gagarumar gudunmawa ga ilimin addinin musulunci a Najeriya. An haifi Sheik Dr Alhassan Saeed a wani gari da ake kira Mekekiya a kusa da wani kauye da ake kira Mai Zuwo a ƙaramar hukumar Sule Tankarkar a ta Jigawa a shekarar 1956, iyayensa na daga cikin waɗanda suka fara zuwa garin.[1]
Sheikh Dr Alhassan Saeed Adam Jos | |
---|---|
Personal | |
Haihuwa | 1956 |
Mutuwa | 05 ga Afrilu 2017 (Shekaru 61) |
Addini | Musulunci |
Dan kasan | Nigeria |
Gida | Jos |
Kabila | Hausa |
Education | PhD |
An san shi da | Da'awah |
Karatu.
gyara sasheMalam ya fara karatunsa a kauyen Ɗan Kama dake ƙaramar hukumar ta Sule Tankarkar amma saboda hali na rashin yarda da boko da da yawa daga cikin iyaye ke yi a wancan zamani yasa babansa ya cire shi daga makarantar ya maida shi makarantar allo a Jobi cikin jihar Kano gurin wani malami mai suna Malam Adamu Jobi, wanda a wannan lokaci babu wani malami kamarsa a wannan yankin, daga nan wani malami ya ɗauke shi zuwa Jos inda ya haɗu da wani malami mai suna malam Muhammad ɗan uwan malam Adam na Jobi anan ya cigaba da karatu a gurinsa ya kuma cigaba da karatun boko.
A shekarar 1972 wani malami ya nemi da suje Maiduguri da suka je can ya haddace Alkur’ani a shekara guda, daga nan kuma ya dawo Jos ya cigaba da karatunsa a gurin wasu malamai daga cikinsu akwai:
- Malam Usman Misau
- Malam Muhammad dan yayar mahaifiyarsa
- Malam Audu Alkalin Shandam
A 1975 lokacin da gwamnati ta kirkiro Universal Basic Education (UBE) malam ya fara karantarwa, daga bisani ya daina karantarwa ya koma makaranta. A shekarar 1979 ya fara Arabic Teachers College Katsina, inda ya gama a 1984/85 ya fito da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa a wannan shekarar har aka bashi kyauta.
A shekarar 1987 malam ya koma Jami'ar Bayero dake Kano inda ya yi diploma a Hausa, Arabic da Islamic Studies. Bayan ya gama sai ya koma Jamiar Jos inda ya yi digiri a Hausa Arabic and Islamic Studies. A shekarar da ya gama Jami'ar Jos ne wasu larabawa daga kasar Saudiya suka zo don shirya bita ga masu karatun addini, malam yaje gaishesu sai suka nemi daya zo ya halarci wannan bita, malam ya halarci bitar inda yazo na biyu, sai larabawan suka ba shi shawara ya cike fam don yin karatu a kasar Saudiya, a nan ne ya yi digirinsa na biyu a tsangayar Alkur’ani.
Bayan ya gama digirinsa na biyu a kasar Saudiya sai ya dawo Jami'ar Jos ya sake wani digiri na biyun, daga baya kuma a shekarar 2007 ya koma Jamiar Usman dan Fodio ya yi digiri na uku (PhD).
Gudumawarsa wajen karatu da karantar da al'umma.
gyara sasheMalam ya share rayuwarsa wajen karatu da karantarwa da yada sunnar Annabin rahama (SAW), ko a ranar da zai bar duniya saida ya karantar da littafin Atttargib Wattarhib na Imamul Munziri (karatun da yake ma take da hikimar safiya).
Malam ya rayu cikin Alkur’ani ya kuma koyar duk bayan sallar Asubahi ko Magriba matukar dai yana gari kazo kofar gidansa zaka same shi yana karanta Alkur’ani ko kuma yana karantarwa. Shine farkon wanda ya fara buɗe halka ta Alkur’ani a garin Jos a layin Mudi na Garba kusa da gidan malam Lawal Maka, mutane sama da 500 sun haddace Alkur’ani a wajensa.
Ba nan kawai malalm ya tsaya ba, ya rike mukamai da yawa da bada gudumawa don cigaban addinin musulunci, daga ciki akwai:
- Shine shugaban kwamitin ilimi da ilimantarwa na kungiyar IZALA
- Shugaban masu bada fatawa na Jama'atu Nasril Islam na jihar Filato
- Mataimakin shugaban shirya gasar musabakar Alkur’ani na jihar Filato
- Ta sanadiyarsa aka gina Shool for Higher Islamic Studies dake sarkin Mangu, wanda yanzu take hannun su Sheik Sani Yahya Jingir
- Shine matashin ahlussunna na farko daya fara tafsirin Alkur’ani acikin a garin Kano a kofar gidan baba Iliya inda Malam Aminu Ibrahim Daurawa ke karatu a yanzu, lokacin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ne mai ja masa baki
- Shine wanda ya fara kirkiro makarantar addini na mata sanda aka kafa kungiyar IZALA
Mu'amalarsa da yan uwansa da sauran al'umma
gyara sasheMalam ya kasance mutum mai kyakkyawar dabi'a ga yan uwansa da sauran al’umma da yake tare da su, mutum ne mai hakuri da juriya bisa abun da aka masa, inda za a masa abu na cutarwa kace zaka rama mai kokarin hana mutum yake yi yace a barsu da Allah.
Malam ya kasance mai kyakkyawar mu'amala da sauran abokansa na da’awa, duk wani abokin da’awa da suke tare da shi zaka samu yana fadan alakairi akansa domin sun san cewa mutum ne mai basira da hangen nesa, baya gaggawar bada fatawa akan addini akan abin da bai sani ba. An sha masa tambaya yace bai sani ba a bari sai ya tambayi malamansa su ba shi amsa.
Littafan da ya karantar a lokacin rayuwarsa
gyara sasheMalam ya karantar da littafai da dama a rayuwarsa daga ciki akwai;
- Bulugul Maram
- Riyadussalihin
- Sahihul Bukari
- Kitabuttauhid
- Muwadda
- Risala na Abi Zaidul Kairawani
- Wasu littafai da suka shafi lugga
- Attargib Wattarhib
Rubuce-rubucensa
gyara sasheMalam ya yi rubuce da dama daga ciki akwai nasihatu dalibu li alimul arbab, bidayatu dalib fi ilmul tajwid (wanda ake karantarwa a duk makaratun IZALA musamman makaratun IZALA bangaren Sheik Sani Yahya jingir.
Dalibansa
gyara sasheMalam yana da dalibai da yawa da suka yi karatu a gunsa daga cikinsu akwai:
- Malam Shehu Sulaiman (wanda ya wakilci Najeriya a gasar karatun Alkur’ani da aka yin a duniya a kasar Saudia)
- Malam Sani Ahmad (yaje musabakar Alkur’ani na kasa da ake shiryawa a Usman dan Fodio)
- Malam Ibrahim Idris Darussa’ada
- Muhammad Nuru Kalid (tsohon limamin masallacin yan majalisa dake Apo Abuja)
- Dr Abdurrahman Idris (Malami a Aminu Kano College for Legal and Islamic Studies)
- Gwani Muhammad Adam Alkadi (dan London)
- Malam Mika’il Muhammad Mika’il
- Malam Salihu Fari
- Malam Ibrahim (Abu Farhan)
- Malam Hashim Sani Hashim
- Muhammad Kabir (Qari'u)
- Malam Sani Ahmad (Abu Rukayya)
Matansa da yayansa
gyara sasheMalama yana da mata guda 4 da yaya 27 da jikoki da yawa, daga cikin yayansa akwai
- Abdulbasid
- Mubarak
- Adda’urrahman
- Najib
- Hamza
- Kadija
- Rukayya
- Ahmad
- Maryam
- Aisha
- Yusra
- Ibrahim
- Aliyu
- Umar
- Mardiya
- Fadl
- Fudail
- Muhammad da sauransu.
Mutuwarsa
gyara sasheMalam ya mutu ranar Laraba 08-07-1438 / 05-04-2017 yana da shekaru 61 a garin Kano, Shugaban Kungiyar IZALA Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ne ya masa salla, dubbannin al’umma sun halarci janazarsa daga Najeriya da kasashen waje.
Manazarta
gyara sashe- ↑ How I succeeded Dr. Gumi - Sheikh Alhassan Jos. Daily Trust (in British English). 4 Sep 2010. Retrieved 02-10-2024.