Sani Yahaya Jingir

Malamin Addinin Musulunci a Najeriya

Sheikh SaniYahaya Jingir malamin addinin Musulunci ne, wanda ke zaune a jihar Filato,[1]. [2] Kuma shi ne Shugaban Majalisar Malaman ƙungiyar nan ta addinin Musulunci, wato Jama'atul Izalatil Bid'ah Wa'Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a ƙarƙashin jahar Jos .[3][4] A ranar 25 ga watan Mayun shekara ta dubu biyu da Sha biyar 2015, an zaɓe shi a matsayin shugaban majalisan ne bayan an yanke shawara a wani taron majalisa a Jos da manyan shuwagabanninta suka yi, wanda majalisar dattawan Ulama’un ta yi, yayin da Sheikh Alhassan Saed Adam ya zama mataimaki, an yi zaɓen ne lokacin da majalisar ta rasa shugabanta Sheikh Isma'il Idris Zakariyya.[5].

Sani Yahaya Jingir
Rayuwa
Haihuwa Jos
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sani Yahaya Jingir
Shaik sani yahya jingir
Shek Sani yahaya jingir

Jingir yana yin tafsirin watan Ramadana na shekara-shekara ne a cikin garin Jos,[6] yana ɗaya daga cikin manya manyan malamai a Arewacin Najeriya. Jingir ya yi wa'azin koyarwa kan mahimmancin fa'idar ilimantarwa a tsakanin dukkan mutanen biyu,[7] Jingir ya yi fatali da cewa duk wanda ya haɗa Ibrahim Inyas tare da Allah a cikin bautansa toshi Kafiri ne.[8] Jingir yana nuna mahimmancin yin azumin sitta shawwal wato azumin da akeyi guda shida bayan gama azumin watan Ramadana.[9] Jingir ya yi ƙira ga gwamnatin Najeriya da tayi duba ga abin da ya faru a kasar Saudi Arebiya a lokacin aikin Hajji a ranar 24 ga watan Satumbar shekara ta 2015,[10] ta dauki kwararan matakai don hana aukuwar irin wannan taron haɗari a gaba. Jingir ya kuma yi ta wa'azi tuƙuru a kan Boko Haram saboda kafircewansu na suna yin Jihadi ba bisa ƙa'idar da Musulunci da Shari'ah suka tsara ba,[11][12] Jingir a lokacin wani bikin buɗe masallacin Juma'ah [Mosque] a saman Dutsen Zinariya a arewacin Jos, Ya gargaɗi masu satar mutane a duk fadin ƙasar da su nemi gafarar Allah, su tuba, haka ma zai shirya addu’o’i na musamman da azumin har Allah Ya shafe su,[13] wasu mutane sun gaza wajan yunƙurin kashe shi bayan an biya shi Naira dubu 500.[14][15][16][17][18].

Manazarta

gyara sashe
  1. https://blueprint.ng/sheikh-jingir-now-plateau-ulamau-council-boss/
  2. https://www.nigerianbulletin.com/tags/sheik-sani-yahaya-jingir/
  3. Blueprint (2015-11-25). "Sheikh Jingir now Plateau Ulama'u Council boss". Blueprint (in Turanci). Retrieved 2020-04-14.
  4. Samfuri:Cite. web
  5. "Jos". BBC News Hausa. Retrieved 2020-04-14.
  6. Tilde, Lawal Umar (2019-05-06). "Ramadan 2019:Jingir Ya Kaddamar Da Tafsiri Da Jan hankalin Malama Da 'Yan Kasuwa". Leadership Hausa Newspapers. Retrieved 2020-04-14.
  7. Shittu, Muhammad Tanko (2019-05-06). "Ramadan Tafsir: JIBWIS harps on women education, deploys 533 preachers". Blueprint (in Turanci). Retrieved 2020-04-14.
  8. Musa, Aisha (2018-04-17). "Nyass ba Allah ba ne, masu danganta shi da Allah sun kafirta - Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir". Legit.ng - Nigeria news. Retrieved 2020-04-14.
  9. "Benefits of Sitta Shawwal Fast, by Sheikh Sani Yahaya". Daily Trust (in Turanci). 2016-07-08. Retrieved 2020-04-14.[permanent dead link]
  10. "Hajj Disaster: Sultan wants Saudi to improve safety during Hajj". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2015-09-26. Retrieved 2020-04-14.
  11. "Babban Taron Wa'azin Kungiyar Izala A Abuja". www.voahausa.com. Retrieved 2020-04-14.
  12. Triumphnews, The (2019-11-19). "Muslims expected to earn from legitimate means – Sheikh Jingir". THE TRIUMPH (in Turanci). Retrieved 2020-04-14.[permanent dead link]
  13. "JIBWIS threatens to spiritually destroy kidnappers". TODAY (in Turanci). 2019-05-03. Retrieved 2020-04-15.
  14. Mustapha, Olusegun (2015-07-10). "'Naira dubu 500 aka ba mu mu kashe Sheikh Sani Yahaya Jingir'". Aminiya (in Turanci). Archived from the original on 2021-05-07. Retrieved 2020-04-14.
  15. Paden, John N. (2012). Postelection Conflict Management in Nigeria: The Challenges of National Unity (in Turanci). School for Conflict Analysis and Resolution, George Mason University. ISBN 978-0-9850966-0-1.
  16. Thurston, Alexander (2016-09-22). Salafism in Nigeria (in Turanci). Cambridge University Press. ISBN 978-1-107-15743-9.
  17. Chesworth, John A.; Kogelmann, Franz (2013-11-25). Sharīʿa in Africa Today: Reactions and Responses (in Turanci). BRILL. ISBN 978-90-04-26212-6.
  18. Rubin, Barry M. (2010). Guide to Islamist Movements (in Turanci). M.E. Sharpe. ISBN 978-0-7656-4138-0.